ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, November 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ba Zai Yiwu A Shafawa Amfanin Allurar Rigakafin Sin Bakin Fenti Ta Hanyar Kitsa Karya Ba

by CMG Hausa
3 years ago
Sin

A halin yanzu, kasar Sin tana kyautata manufofinta na kandagarkin annobar cutar COVID-19, matakin da ya samu maraba daga dukkanin sassan duniya.

Amma wasu ‘yan siyasa, da kafofin watsa labarai na kasar Amurka, suna sake shafawa alluran rigakafin cutar da kasar Sin ta samar bakin fenti, kuma yunkurinsu shi ne musunta kokarin da kasar Sin take yi kan aikin dakile yaduwar cutar, tare kuma da sayar da karin magungunan kamfanonin kasar a kasar Sin.

ADVERTISEMENT
  • Jawabin Murnar Shiga Sabuwar Shekara Na Shugaban CMG 

Kawo yanzu, adadin nau’ikan rigakafin kasar Sin ya riga ya kai 13, wadanda ake samarwa daga fasahohi iri 4. Kaza lika nazarin kimiyya, da sakamakon rigakafin da aka samu sun nuna cewa, allurar rigakafin kasar Sin sun dace da ma’aunin hukumar kiwon lafiyar duniya WHO, wato suna magance kamuwa da cutar, da magance kamu da nau’ikan ta masu tsanani, da kuma magance mutuwa sakamakon kamuwa da cutar.

Bugu da kari, sakamakon gwajin shi ma ya nuna cewa, rigakafin kasar Sin yana da inganci da tsaro, kuma tuni an riga an yi alluran ga Sinawa da yawan su ya kai kaso 92.9 bisa dari. Ciki Sinawan har da tsofaffi wadanda shekarunsu suka kai sama da 60 da yawan su ya kai kaso 90 bisa dari. Ban da haka, kasar Sin ta shiga shirin COVAX, inda ta samar da rigakafi biliyan 2.2 ga kasashen duniya sama da 120.

LABARAI MASU NASABA

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

Allurar rigakafin COVID-19, makami ne na shawo kan cutar, ba makamin siyasa da ake amfani da shi domin shafawa sauran kasashe bakin fenti ba, don haka ya dace irin wadannan ‘yan siyasar Amurka, su cika alkawarin da suka yi, na samar da rigakafi kyauta ga masu bukata, ta yadda za su taka rawar da suke iyawa, a aikin kandagarkin cutar a kasar su, da ma a fadin duniya baki daya. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95
Daga Birnin Sin

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

November 16, 2025
Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku
Daga Birnin Sin

Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

November 16, 2025
Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta
Daga Birnin Sin

Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

November 16, 2025
Next Post
Gwamnatin Gombe Ta Nada Sabbin Shugabannin Rikon Kananan Hukumomi

Gwamnatin Gombe Ta Nada Sabbin Shugabannin Rikon Kananan Hukumomi

LABARAI MASU NASABA

Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja

Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja

November 16, 2025
Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su

Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su

November 16, 2025
Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

November 16, 2025
Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara

Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara

November 16, 2025
Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

November 16, 2025
Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

November 16, 2025
An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing

An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing

November 16, 2025
Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30

Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30

November 16, 2025
Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle

Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle

November 16, 2025
DSS

Hukumar DSS Ta Kama Wani Kan Zargin Ƙerawa Da Rarraba Makamai A Filato

November 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.