Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Jurgen Klopp ya ce ba zai bar kungiyar ba sai idan an kore shi, sannan ya kuma yi karin haske kan canje-canje da zai yi a kungiyar.
Klopp ya yi wannan kalaman ne bayan kasa taka rawar gani da Liverpool ke yi, wadda take ta tara a teburin Premier League sannan an bai wa kungiyar tazarar maki 10 a gurbin ‘yan hudun farko a teburin babbar gasar kwallon kafa ta Ingila ta kakar nan.
- Zaben 2023: Majalisar Dinkin Duniya Da ECOWAS Sun Yi Sabon Gargadi
- Shagalin Murnar Bikin Bazara Ya Gabatar Da Shirye-shirye Masu Ban Sha’awa Ga Sinawa A Duk Duniya
Klopp ya ce ”Sai dai idan an samu sauyi daga shugabancin kungiyar ko kuma wani gagarumin abu ya faru da ke bukatar canji amma kawo yanzu kamar yadda na sani, sai wani ya bukaci da na bar kungiyar, amma yanzu ina nan daram.”
Ya kara da cewar ”Hakan na nufin cewar mun kai lokacin da za mu sauya wasu abubuwan kuma za kuma mu duba hakan, amma hakan sai nan gaba, zuwa karshen kakar nan. Amma ba a wannan lokacin ba.”
Ya ce ”Ina da lokacin da zan yi tunani sosai, ya kamata mu kara kwazo fiye da yadda muke a yanzu.”
Klopp ya ce abune mai wahala idan za su sake yin cefane, bayan daukar dan kwallon Netherlands, Cody Gakpo a Janairu, yayin da ‘yan wasa hudu kwantiraginsu zai kare a karshen kakar nan.
‘Yan wasan sun hada da James Milner da Naby Keita da Aled Odlade-Chamberlain da kuma Roberto Firmino wadanda kuma suna daya daga cikin ‘yan wasan da kungiyar take takama da su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp