Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce ba zai magana dangane da dambarwar da ke cikin jam’iyyar tasu a Kano ba.
Kwankwaso, ya shaida wa Æ´an jarida hakan bayan wani taron karbar ‘yan jam’iyyar APC da suka sauya sheka zuwa NNPP a gidansa da ke Miller road a kano.
- Xi Ya Bukaci Bunkasa Tsarin Dabarun Soja Na Zamani
- Jirgin Ƙasa Na ‘Red Line’ Ya Fara Aiki Yau A LegasÂ
“Ba na son na tattauna a kan wannan batun. Ka da ku tsoma ni a cikin al’amarin da bai kamata na shiga ciki ba. Shugaban jam’iyya ya riga ya yi magana saboda haka za ku iya tuntubar sa.”
Rikicin jam’iyyar NNPP a Kano dai ya janyo dakatar da sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Baffa Bichi da kwamishinan sufuri, Muhammad Diggol.
Dakatarwar ta zo ne jim kadan bayan da gwamna Abba Kabir Yusuf ya jogoranci sasanci tsakanin sakataren gwamnatin, Abdullahi Bichi da wasu ‘an mazabarsa.
Bichi dai ya nesanta kansa daga zargin kafa wata kungiya mai suna “Abba Tsaya da Ƙafarka” da ke fafutukar raba gwamna Abba Kabir Yusuf da uban gidansa, Rabi’u Musa Kwankwaso.