Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Mohamed Salah ya ce babu wata alama dake nuna tsawaita kwanginsa da kungiyar tasa, kuma da ”kamar wuya” hakan ta kasance saboda har yanzu babu wata magana mai karfi tsakaninsa da shugabannin kungiyar duk da cewa magoya baya suna ta kiraye-kirayen cewa ya kamata ya sake sabon kwantiragi a kungiyar wadda take mataki na daya a teburin gasar Premier.
Salah, dan asalin kasar Masar ya shiga wata shidan karshe na kwantiraginsa, kuma a yanzu zai iya tattaunawa da kungiyoyin da ba na Ingila ba, kan makomarsa idan kwantiraginsa ya kare a wannan kaka inda a kwanakin baya a ke ci gaba da danganta dan wasan da komawa kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German, sannan kungiyoyi daga kasar Saudiyya ma suna bibiyar halin da yake ciki a Liberpool din.
Dan wasan mai shekara 32 a duniya ya koma Liberpool ne daga Roma a shekarar 2017, kuma a wannan kaka ya zura kwallo 20 a duka wasannin da ya buga wa kungiyar a bana, lamarin da ya taimaka wa kungiyar darewa teburin Premier da na Gasar Zakarun Turai kuma a yanzu haka dan wasan ne kan gaba a yawan zura kwallo a gasar Premier, inda ya ci 17, uku fiye da Erling Haaland na Man City.
Da aka tambaye shi, ko yana tunanin wannan ce kakarsa ta karshe a Anfield? sai ya amsa da cewa ”ya zuwa yanzu dai haka ne, saura wata shida domin babu alamun ci gaba da zamansa a kungiyar, Salah, wanda a baya ya buga wasa a kungiyoyin Chelsea da Basel da Fiorantina ya kara da cewa da alama ba za su daidaita ba, amma dai suna jira su gani shi da wakilansa.
Sai dai a baya-bayan nan Salah na yawan magana da kafafen yada labarai game da makomarsa a Liberpool, sannan a watan Satumbar shekarar da ta gabata ma, lokacin da Liberpool ta doke Manchester United, dan wasan ya ce ya buga wasan ne tamkar wasansa na karshe a Old Trafford, sannan ya maimaita kalaman nasa a lokacin da suka doke Manchester City a watan da ya gabata.
Shi ma kaftin din kungiyar, Birgil ban Dijk da Trent Aledander-Arnold kwantiraginsu zai kare a karshen wannan kakar kuma ana danganta shi da komawa kasar Saudiyya da buga wasa ko kuma kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, har ila yau ana alakanta Aledander-Arnold, wanda shima kwantiranginsa zai kare a kungiyar ta Liberpool da komawa kungiyar Real Madrid.