Sanata Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Tarayya, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta guji ƙara wa ’yan Nijeriya da ke cikin ƙuncin rayuwa haraji.
A wata hira da ya yi a shirin Prime Time na gidan talabijin na ARISE, Ndume ya bayyana adawarsa ga ƙudirin ƙarin haraji da ke cikin dokokin sake fasalin haraji da aka gabatar, yana mai cewa wannan mataki zai kara wa talakawa nauyi.
- Da Gangan Aka Rikirkita Tsarin Zaben Nijeriya Domin A Samu Damar Yin Magudi – Sanata Ndume
- Ko Za A Kore Ni Daga APC Ba Zan Daina Fadar Gaskiya Ba – Ndume
Sanatan ya yi nuni da cewa masu rufin asiri cikin ƴan Njeriya yana raguwa sosai, inda da yawa ke fadawa cikin talauci. Ya ce ƙarin haraji a wannan yanayin tattalin arziƙi bai dace ba, musamman ganin yadda jama’a da dama ke shan wahala wajen ciyar da kansu. “Ko kana da shi, ko kuwa ba ka da shi,” in ji shi, yana mai jaddada cewa ya kamata a dora nauyin haraji a kan attajirai da kamfanoni masu hannu da shuni.
Ndume ya sha alwashin yin kamfen kan duk wani ƙarin haraji da zai shafi masu karamin karfi, musamman a yankin Arewa inda talauci ya fi yawa. Ya nemi hukumar tattara haraji ta mayar da hankali kan masu hannu da shuni, yana cewa,
“Kada ku ɗora wa mutane da ke cikin ƙunci haraji; ya kamata hukumar tattara haraji ta mayar da hankali kan wadanda ya kamata su biya.”