Daya daga cikin manyan mawaka da suka yi tashe a shekarun baya a masana’antar Kannywood, Adamu Nagudu ya yi magana kan batutuwa da dama da suka hada da masana’antar Kannywood a da da yanzu da kuma sauran batutuwa da suka shafi rayuwarsa ta waka.
Nagudu a hirar da ya yi da jarumar Kannywood Hadiza Gabon a cikin shirinta mai suna ‘Gabon’s Room Talk Show’ ya fara magana ne a kan yadda ya samu kanshi a matsayin mawakin Kannywood duk da cewar shi malamin makarantar Islamiyya ne a birnin Jos kafin ya dawo Kano da zama.
- Burina Fim Ya Zama Sana’a A Nijeriya Kamar Indiya Da Amurka – Mustapha Nagudu
- Karewar Basira A Wakokin Soyayya Ta Sa Na Daina Yin Su – Mahmud Nagudu
Inda ya ce Allah madaukakain Sarki shi ne kadai ya isa ya tsarawa dan adam yadda rayuwarshi za ta kasance, saboda haka ba abin mamaki ba ne ace malamin makarantar Islamiyya wanda ya ke da dalibai masu yawa a kasan shi daga baya kuma ya samu kanshi a matsayin mawakin Kannywood, wannan iko ne na Allah kawai wanda yake abinda ya so ga wanda ya so a kuma lokacin da ya so.
Nagudu ya ci gaba da cewa a baya sunan shi Sayyadi wanda ya samu asali sakamakon karantar da kalibai da yake yi a Jos kafin ya zo Kano, amma bayan ya zo Kano sai ya fara aiki a wani kamfani da ake kira Nagudu Inbestment tare da abokina Mahmud Nagudu.
A kan tsohuwar alakar shi da jaruma Jamila Nagudu, Adamu ya ce a can baya tun kafin Jamila ta shigo harkar Kannywood muke tare da ita wanda har ya kai ga mun sako manya dangane da batun aurenmu, amma daga baya wasu suka hure mata kunne a kan a wancan lokacin tana da wata fuska ko lokaci da ya kamata ta fara harkar fim, hakan yasa ta ce ba za ta yi aure ba a wancan lokaci.
Da aka tambaye shi minene sirrin nasara ko daukakar da ya samu a masana’antar Kannywood, Adamu ya ce babu wani sirri akan wannan nasara da ya samu illa biyayya ga iyaye, domin kuwa a duk lokacin da iyayenka suka yi maka addu’ar samun nasar Insha Allah ba zaka wofanta ba muddin kana kyautata masu inji shi.
Adamu Nagudu ya ci gaba da cewa masana’antar Kannywood wadda ta ke da dadadden tarihi, ta canza matuka a bangaren tarbiyya da girmama juna a tsakanin jarumai a masana’antar ba kamar yadda muka yi a baya ba, domin a wancan lokacin akwai girmama juna a tsakanin manya da kanana a masana’antar ba kamar yanzu da zaka ga yaro yana nuna da shi da babba duk daya ne saboda dukansu mawaka ne ko kuma dukansu jaruman fim ne.
Haka kuma canjawar da Kannywood ta yi akwai ta barayin kasuwanci, domin a wancan lokacin idan ka saka kudadenka a masana’antar ta kowane fanni kama daga waka da masu shirya fina-finai, zaka samu riba matuka, ba kamar yanzu ba domin kuwa ni ba zan iya zuba kudadena a yanzu kamar yadda na zuba a lokacin baya ba in ji shi.
Daga karshe Adamu Nagudu ya ce ko alama bai yi da nasanin shigarsa masana’antar Kannywood duk da cewar shi malamin makarantar Islamiyya ne kafin zuwansa Kannywood, domin kuwa babu abinda ya canza a matsayina na Malami kuma dalibi a makarantar Islamiyya, domin har yanzu duk ranar da Allah ya kaini Jos ni kan yi kokarin zuwa makarantar domin bayar da tawa gudunmawar a kowane fanni.