A yayin da zaben 2023 ke kara tunkaro wa, shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayar da tabbacin ba zai mara wa dan takarar shugaban kasa na jamiyyar PDP, Atiku Abubakar, baya ko wani dan takarar shugaban kasa ya kyale dan takarar shugaban kasa na jamiyyar APC mai mulki ba, Ahmed Bola Tinubu ba.
Buhari wanda ya bayyana hakan a jiya Laraba, ya mayar da martani ne kan jita-jitar da ke kara karuwa ta cewa, wasu Jigajigai a Jam’iyyar APC za su mara wa Atiku baya a mai makon su mara wa Tinubu baya.
- Rikicin PDP: Bayan Ganawar Tinubu Da Wike A Landan, Ba Shiri Atiku Ya Garzaya Birtaniya
- PDP Ta Shiga Fargaba Bayan Wike Ya Yi Ganawar Sirri Da Tinubu
Har ila yau, baya ga Atiku da Tinubu, ana jita-jitar Jigororin na APC, za su mara wa ‘yan takarar shugaban kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP da kuma dan takarar shugaban kasa na jamiyyar LP Peter Obi.
An ruwaito wasu daga cikin Jigororin PDP da ke yi wa Atiku biyayya sun shelanta cewa, wani bangaren na fadar shugaban kasa na zawarcin Atiku bisa aniyar mara masa baya don tunkarar zaben na ranar 25 ga watan Fabirairun 2023.
Buhari, a cikin sanarwar da mai magana da yawun fadar shugaban kasa ya fitar, Mal. Garba Shehu, ya ce, Buhari zai mara wa dan takarar shugaban kasa wanda APC ta tsayar a 2023.
Sanarwar ta ce, fadar shugaban kasa ba ta da wani dan takara da ya shige na APC, inda sanarwar ta kara da cewa, Buhari zai kuma ci gaba da mara wa APC baya.
A cewar sanarwar, Shugaba Buhari ya kuma umarci duk wadanda suke a fadar ta shugaban kasa da su yi watsi da irin wannan maganar da ke da sarkakiya don gudun kar a lalata tafiyar APC da kuma ta gwamnatin Tarayya, don gudun kar ‘yan adawa su yi amfani da hakan, a matsayin wani makami na siyasa.