Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi karin haske kan kalaman da ya yi kan jami’o’in gwamnatin tarayya a babban taron kungiyar lauyoyin Nijeriya (NBA) na shekara-shekara da ya gudana a otal din Eko, jihar Legas.
Atiku wanda yana daya daga cikin wadanda suka halarci taron a ranar Litinin din da ta gabata, ya bayyana yadda suka hadu da wani farfesa a jami’ar tarayya da ke Lokoja a jihar Kogi.
Daily trust ta ce, Atiku Ya ce, Gwamnatin Tarayya ba ta da kayan aiki don gudanar da ingantattun jami’o’in tarayya a kasar nan.
“Na yi jayayya da wani malamin jami’a daga Jami’ar Tarayya, Lokoja. Ya ce ya karanta a cikin takardar manufofina cewa na yi niyyar mayar da Jami’o’in tarayya karkashin gudanarwar Gwamnatin jihohi. Ta yaya zan yi haka? Na ce: ‘Malam Farfesa, ka san cewa rukunin farko na jami’o’inmu na karkashin gwamnatocin yanki ne?’ Ya ce, ‘Eh’. Na ce ‘Su wane ne wadanda suka gaje gwamnatin yankin?’ Ya ce: ‘jihohi’.
“Na ce yaran da muke turawa Amurka ko Ingila su yi Karatu, su waye suka mallaki wadannan jami’o’in? Galibi kamfanoni masu zaman kansu. To, me ya sa kuke tunanin ba za mu iya yin hakan a nan ba? Ba mu da kudi.”
Sai dai a wata sanarwa da Paul Ibe, mai baiwa dan takarar shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai ya fitar, ya ce Atiku ya yi magana ne kawai kan shirinsa na mika ragamar mulki ga sassan gwamnatin tarayya.
“Rahoton karya ne, ba gaskiya ba ne, ba shi da tushe, kuma ba gaskiya ba ne abin da aka rahoto cewa Atiku Abubakar ya fada yayin da yake amsa tambaya kan batun raba madafun iko.