Tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon Sanatan Kano ta tsakiya, Ibrahim Shekarau, ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su fifita sahihancin ‘yan takara maimakon batun karɓa-karɓa da ya mamaye zancen zaɓen 2027.
Da yake magana a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels Television’s (Sunday Politics), Shekarau ya jaddada cewa muhawara kan asali ko yankin da shugaban ƙasa ya fito ba shi da alaka da ingantaccen ko nagartaccen shugabanci.
- Fahimtar Damammakin Da Sin Za Ta Samar Wa Duniya A Shekarar 2025 Daga Babban Taron Ayyukan Tattalin Arzikin Kasar
- ‘Yan Nijeriya Za Su Kayar Da APC A 2027 Kamar Yadda Aka Yi Wa NPP A Ghana – PDP
“Ya kamata dukkan jam’iyyun siyasa su mayar da hankali wajen gabatar da ’yan takarar da suka fi dacewa. Abin tambaya ga ‘yan Nijeriya shi ne: ‘wanne shugaban ne zai yi jagoranci nagari a Nijeriya?”
Inji Shekarau.
Ya ci gaba da cewa, “Ƙalubalen shi ne jam’iyyu su bai wa ‘yan Nijeriya ’yan takarar da suka cancanta. ”
Tsohon Sanatan na Kano ta tsakiya ya kuma yi tsokaci kan gwamnati mai ci, inda ya bukaci gwamnatin shugaba Bola Tinubu da ta saurari ra’ayoyin ‘yan Nijeriya da kuma magance matsalolin da suka shafi tattalin arziki da shugabanci.
Kalaman na Shekarau sun nuna yadda ake ci gaba da yin kiraye-kirayen a sauya fasalin siyasar Nijeriya wajen ba da fifikon cancanta da rikon amana maimakon kallon yankin da shugaban kasa zai fito ko ya fito.