Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya zargi tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da jam’iyyar APC da hannu wajen haifar da rashin tsaro a Nijeriya don cimma manufofin siyasa kafin zaɓen 2015.
Yayin da yake magana a shirin siyasa na gidan talabijin na Channels, Baba-Ahmed, ya ce shugabannin APC sun ƙirƙiri tsoro da rabuwar kawuna domin hana mulkin Shugaba Goodluck Jonathan yin nasara, tare da tabbatar da cewa Muhammadu Buhari ya lashe zaɓen 2015.
- Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP
- Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP
Ya zargi El-Rufai da shirya makirci, yana mai cewa yana cikin tsarin da ya haifar da rikice-rikice a Arewa.
Haka kuma, Baba-Ahmed ya danganta tashin hankalin da ya ɓarke a Kaduna da wasu sassan Arewa a 2011 da maganganun Buhari na lokacin yaƙin neman zaɓe inda ya yi nuni da cewa “jini zai zuba.”
Ya ƙara da cewa an shigo da ‘yan tawayen ƙasashen waje cikin Nijeriya a lokacin don tayar da tarzoma, kuma wannan ne tushen matsalolin tsaro da ake fuskanta a yau.
Baba-Ahmed, ya bayyana cewa, abin da danginsa suka fuskanta a hannun masu garkuwa da mutane a bara ya tabbatar masa da cewa rashin tsaro a yanzu yana da nasaba da siyasa.
Ya kuma danganta kisan jama’ar da aka yi wa mabiya Shi’a a Zariya a shekarar 2015 da wani shiri na gwamnati don murƙushe masu sukarsu a wancan lokaci.
Ya jaddada cewa El-Rufai da jam’iyyar APC ba za su iya tserewa daga alhakin halin da Nijeriya ke ciki na rashin tsaro ba.