Cikin wannan jamhuriyar siyasa ta hudu a wannan Kasa, wadda ta faro daga Shekarar 1999 zuwa yau (2023), ta tabbata cewa, ba a sami wani shugaba turun bashi a matakin kasa tamkar Buhari ba, sai dai a matakin jiha ne ake da mutane irinsu El-Rufa’i, Ganduje da ire irensu.
Cikin jamhuriyar ta hudu zuwa yau (2023) kasar nan ta yi shugabanni hudu (4) ne cifcif : shugaba Olusegun Aremu Obasanjo (1999-2007), sai shugaba Umaru Musa “Yar’adua (2007-2009), sai shugaba Goodluck Ebele Jonathan (2009-2015), sai shugaba na yanzu da ke hada komatsansa shi da tawagarsa, akan hanyarsu ta yin ban kwana da Dutsen Haso, shugaba Buhari (2015-2023). Wata kididdiga ta nuna cewa, cikin Shekarar 2006, wato lokacin da Obasanjo ke mulkar wannan Kasa, shi ne wani shugaba na farko a kaf cikin nahiyar Afurka, wanda ya fara yunkuri gami da warware wani kunzumin bashi da kasashen ketare ke bin Kasarsa, karkashin wani yunkuri da aka yi, na tallafar Kasashe matalauta da kuma Kasashen da basuka suka yi musu katutu!.
- Samar Da Daidaito A Tsarin Hada-hadar Kudi A Bankunan Nijeriya
- Yawan Hatsi A Kasar Sin Zai Ci Gaba Da Karuwa A Bana
A wancan lokaci ne, gwamnatin ta Obasanjo, ta yi wani irin namijin kokari, inda ta saukewa wannan Kasa zunzurutun taragon bashi har na dalar Amurka biliyan goma sha takwas ($ 18b), akan hanyarta na nuna kyakkyawan yunkuri da take shi na son sauke nauyin basukan da ke kanta, inda wannan yunkuri zai ba da damar a yafe mata sauran basuka na dalar Amurka kusan biliyan talatin ($ 30b) da hukumomi na ketare irinsu London da Paris Clubs ke bin Kasar ta Najeriya.
Babu shakka, cikin wannan jamhuriyar siyasa ta hudu, ba a sami wani shugaba da ya tasamma yi wa runbum bashi na wannan Kasa ta Nijeriya raga-raga ba tamkar Baban Iyabo, Obasanjo, haka a daya hannun, a dai cikin jamhuriyar, ba a sami wani shugaba a matakin taraiya da ya durkusar ko gurfanar da wannan Kasa rike da kokon bara ga gagga gaggan kungiyoyin tatsar jini da ba da lamunin bashi na Duniya tamkar Buharin Daura ba. Sabanin yadda Sanata Solomon Adeola ke fadi wai cewa, sauran gwamnatoci da suka gabata ne suka yi uwa da makarbiya wajen ciyowa wannan Kasa mamakon bashin da ka jibge a kanta. Ko kadan! Domin kuwa binciken da jaridar Premium Times ta yi a watan Okotoban Shekarar 2021 (October, 2021) ya karyata wancan ikirari na Sanata Adeola, tare da gabatar da wasu tarin hujjoji tiryan tiryan.
Da mutum zai dan kara dora lissafi akan waccan kididdigar basukan ketare da aka ciwowa wannan Kasa karkashin mulkin Buhari a Shekarar 2020 zuwa wannan Shekara ta 2023 da muke ciki, babu shakka sai raskwanar kwakwalwar kansa ta dauki dumi ko zafi, duba da irin karin lallaftun tarin basuka na hawan kawara da ake kan ciwowa Kasar dare da rana babu kakkautawa.
Haka suma basukan gida da wannan Kasa ke kan lakumewa, hakika sun fi kazanta karkashin mulkin na Buhari a dai cikin wannan jamhuriyar siyasa ta hudu. Cikin Shekarar 2015, gwamnatin Buhari ta gaji adadin bashin gida daga gwamnatin Goodluck na naira tiriliyan takwas ne da digo takwas (N 8.8tr). Amma a Disambar Shekarar 2020, bashin na gida, ya ninku ne zuwa naira tiriliyan sha shida da digo sifili da biyu (N 16.02tr).
Hatta darajar naira sai da ta kara yin biji-biji ne a karkashin mulkin na Buhari. Cikin Shekarar 2015, adadin naira dari da casa’in da bakwai ne ke yin dala guda. Amma, a farko farkon Shekarar 2020 (December, 2020), dalar Amurka guda, tana daidai ne da naira dari uku da tamanin da daya. Babu shakka, a duk sa’adda tarnakin basukan gida da na daji suka yi wa Kasa katutu musamman a wannan nahiya tamu ta Afurka, za a samu cewa lamuran sabgar kudadenta na neman durkushewa ne kacokan. Ta yadda kimarsu da kuma kwarjininsu zai yi kasa ainun a idon al’umar Duniya ta fuskacin hada-hadar kasuwanci da kuma sha’anin saye da sayarwa.
Ba ya ga irin hadidiyar tarin basuka na gida da na waje da ake fama da su cikin wannan Kasa a matakin gwamnatocin taraiya, yanzu haka wannan annobar bashi na neman zama sunnar gwamnoni a Kasar. Ta tabbata daga sabbin gwamnonin sha bakwai (17) da za su tsinci kansu bisa tsinin mashi a wannan Kasa, akwai sabbin gwamnonin Kano da Kaduna!!! Hakika lamarin Kaduna na da matukar daure kayi.
- Ninkayar El-Rufa’i A Tekun Bashin Ketare
Cikin wata kididdiga da aka yi, wadda ke nuna irin yanayi na tashin tashina da sabbin gwamnoni sha bakwai (17) a wannan Kasa za su tsinci kawunansu ciki bayan an rantsar da su sun kama aiki, sakamakon ciwo mangala mangala ko kwantena kwantena na basukan gida da na ketare da tsoffin gwamnoni suka ciwo da sunan gudanar da aiyukan ci gaba a wadannan jihohin, lamarin wasu gwamnoni ciki har da na Kaduna na da daure kai ainun, inda za a ga yawan basuka na ketare da jihar ta Kaduna ta ciwo ita kadai, ya kere na sama da jihohi tara, cikinsu har da Kano auki. An gabatar da waccan kididdiga ne jim kadan, bayan kammala zabukan gwamnoni da aka yi a Kasa ba da jimawa ba. Ga yadda kididdigar ta kasance;
–Jihar Kano ta ciwo bashin ketare na dalar Amurka miliyan dari daya da tara, da dubu dari hudu da ashirin da biyu da “yankai ($ 109, 422, 176. 85).
–Jihar Katsina ta ciwo bashin ketare na dalar Amurka miliyan hamsin da biyar da dubu dari takwas da ashirin da hudu da “yankai ($ 55, 824,330.35).
–Jihar Kebbi ta ciwo bashin ketare na dalar Amurka miliyan arba’in da biyu da dubu dari hudu da uku da “yankai ($ 42, 403, 327. 93).
–Jihar Niger ta ciwo bashin ketare na dalar Amurka miliyan sittin da tara da dubu dari biyu da sittin da shida da “yankai ($ 69, 266, 186. 30).
–Jihar Jigawa ta ciwo bashin ketare na dalar Amurka miliyan ashirin da bakwai da dubu dari shida da sha daya da “yankai ($ 27, 611, 046. 36).
–Jihar Benue ta ciwo bashin ketare na dalar Amurka miliyan talatin da dubu dari hudu da saba’in da biyu da “yankai ($ 30, 472, 977. 14).
–Jihar Cross Riber ta ciwo bashin ketare na dalar Amurka miliyan sha biyar da dubu dari bakwai da hamsin da hudu da “yankai ($ 15, 754, 975. 33).
–Jihar Akwa Ibom ta ciwo bashin ketare na dalar Amurka miliyan arba’in da shida da dubu dari biyar da sittin da tara da “yankai ($ 46, 569, 647. 22).
–Jihar Taraba ta ciwo bashin ketare na dalar Amurka miliyan ashirin da biyu da dubu dari biyu da tamanin da “yankai ($ 22, 280, 666. 89).
To ko mai karatu ya san bashin ketare nawa ne jihar Kaduna ta yi jan-idon ciyowa ita kadai?;
–Jihar Kaduna ita daya kwallin kwal, ta ciyo bashin ketare ne na dalar Amurka miliyan dari biyar da tamanin da shida da dubu dari bakwai da saba’in da shida da “yankai ($ 587, 776, 219. 18).
Da kuma za ka hada lissafin basukan ketare da wadancan jihohi 17 da sabbin gwamnoni za su amshi ragamar mulkinsu a Watan Mayu maizuwa suka ciwo, sai a iske cewa, sun ciwo bashin dalar Amurka biliyan guda ne da miliyan dari bakwai da hamsin da biyar da dubu dari tara da sittin da takwas da “yankai ($ 1, 755, 968, 311. 36).
Da me da me gwamna Nasiru El-Rufa’i ya yi da irin wadancan madudan kudade shan-kai? Ba zancen gadaji da hanyoyi za ka fi mayar da hankali a bayani ba. Irin wadancan madudan kudade ta bakin masana, indai ba za a saka su cikin aiyukan da za su haihu, su biya basukan da aka ciwo dominsu ba, rashin ranto su ne ya fi alkhairi.