ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, June 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Samar Da Daidaito A Tsarin Hada-hadar Kudi A Bankunan Nijeriya

by Sabo Ahmad
3 years ago
Daidaito

Tsarin yin hada-hadar kudi ta hanyar tura wa, wanda Babban bankin Nijeriya ya fito da shi, ya fito da shi ne domin saukaka hanyoyin kasuwanci da biyan kudi, tsakanin mai saye da mai sayarwa.

An fara wannan tsarin ne, lokacin da aka gabatar da shi, a matsayin hanyar da za dinga yin saye da sayar wa, ta hanyara tura kudi banki da kuma sauran wasu hada-hadar da suka shafi kasuwanci. Ko shakka babu, wannan tsari ne da yakamata a yi maraba da shi, domin ya kawo ci gaban da ya taimaka wajen samun saukin yin kasuwanci ta hanyar tura kudi, da kuma kawar da takura da fuskantar barazana.

  • Amfani Da Brush Wajen Kwantar Da Gashi
  • INEC Ta Bai Wa Zababben Gwamnan Kebbi Takardar Shaidar Lashe Zabe

Duk da kyawawan tsare-tsaren da ake da su, akwai bukatar kara fadada tsarin domin a samu karin wasu hanyoyin hada-hadar kudin a Nijeriya.

ADVERTISEMENT

Idan har za a iya cike wannan gibin, za a samu ci gaba a kan hanyoyin hada-hadar kudin kamar yadda gwamnan Babban bankin Nijeriya Mista Godwin Emefiele, ya nuna,cewa akwai bukayar hadin gwiwa da Hukumar daidaita tsakanin bankuna ta Nijeriya da gabatar da katin kasa na bai-daya. Kwararrau sun bayyana cewa,manufar wannan tsarin shi ne, adana kudaden kasashen waje. Da wannan tsarin ne, tsarin kudaden kasar nan zai iya biyan dala ce kan kasuwancin da aka yi da katin gida ko na kasar waje a wajen kasar nan.

Ko shakka babu,tsarin samar da katin, babban ci gaba ne, saboda wasu dalilai masu yawa, wadanda ba a ambace su ba, kamar taimaka wa wajen rage yawan kudin da za caza. Haka kuma a matakin farko masu kula da tsarin biyan kudin da kuma musamman, Babban bankin Nijeriya, sun tabbatar da cewa, gabatar da wannan tsari da kuma aiwatar da shi zai sama da wasu sababbin damarmaki wajen harkokin kasuwamci wanda kasashe da dama za su ci gaba da amince wa da shi wadanda har su ma za su samar wa da kansu katin domin su shiga tsarin irin wannan tsari na yin amfani da katin biyan kudi.

LABARAI MASU NASABA

Zargin Ɓata Suna: Kwankwaso Ya Yi Barazanar Neman Diyyar Naira Biliyan 10 Kan Wani Malamin Coci

Atiku Ya Soki Tsare El-Rufai, Ya Ce Sharuɗan Belinsa Sun Yi Tsauri

Shugaban Babban bankin ya tabbatar da cewa, tsarin biyan kudin yana da matukar amfani a matsayinsa na wani dandali da ya bude hanyar samun ci gaba a fagen hada-hadar biyan kudi, kadan da matsakaita da kuma hanyoyin kasuwanci. A bisa dukkan alamu tsarin zai taimaka wajen bunkasar tattalin arzikin Nijeriya da wasu kasashen Afirka da ma duniya baki-daya.

Samar da irin wadannan masana’antu da hada kai da su wajen tafiyar da su, da kuma tsarin samar da bankin al’umma na Nijeriya sun taimaka wajen karin fuskantar kalubale kan yadda za a samar da tsarin biyan kudin ta hanyar amfani da kati.

Yana da matukar muhimmanci a samar da katin biyan kudi a Nijeriya wadda ake samun bunkasar tun tsawon shekaru masu yawa da suka wuce, duk da haka da yawa daga cikin ‘yan Nijeriya na fuskantar kalubale wanda haka ya sa suka samu koma-baya a wasu sabbin tsare-tsaren na tafiyar da harkokin kudi. Wannan abu ne wanda za a iya cewa,kamar an gaje shi ne tun tuni wadanda suka hada da yawan kudin da ake kashe wa wajen yin amfani da katin na da, wanda wand aba za iya amfani da shi ba a wasu kasuwannin Nijeriya ba.

Haka kuma kayyade lokacin aikin katin ga ‘yan Nijeriya, domin kada a tsawaita lokacin aikin nasa Babban Bankin Nijeriyar ya nuna cewa, bayan lura da yadda tsare-tsaren ke gudana, zai karfafa yin amfani da katin wajen hada-hadar kasuwancin cikin gida sannan kuma zai warware wasu matsaloli. Wannan tsari ne wanda Emefiele ya bayyana matsayinsa, saboda haka, dole mu dauke shi da matukar muhimmanci.

Yana da matukar muhimmanci a jinjina wa tare da yaba wa gwamnan Babban bankin nijeriyar, musamman kan kokarinsa na aiwatar da wasu sabbin tsare-tsare da suke tafiya kafada da kafada da sauran kasashen duniya. Musamman samar da kati domin yin hada-hadar kasuwancin ciiin gida, ko shakka babu, wannan tsari ne da ake amfani da shi a duniya, wanda yin haka ya kara masa daukakak.

Ta hanyar wannan tsarin Babban bankin,ya shigar da Nijeriya cikin sahun masu amfani da kati. Yanzu haka, kan irin wannan tsarin Nijeriya,na cikin rukunin kasashe irin su, Chana da Rasha da Turkey bugu da kari kuma ita Nijeriya har ta samar da katin kanta.

Wannan kokarin ne na musamman da ya kamata a karfafa domin rage shigowar wasu kasashen duniya domin su baje kolinsu na samar da sabis dinsu a Nijeriya. Abu ne wanda yake a zahiri cewa, hada-hadar kasuwanci a Nijeriya na da yawa,kuma ta kara habaka sosai cikin wadannan shekarun da muke ciki.  Duk da haka akwai kafa da kara ci gaba da bunkasar hada-hadar kasuwancin da biyan kudi ta hanyar tura wa kai-tsaye zuwa asusun wanda aka sayi kayansa

Duk da wadannan sababbin tsare-tsare da da Babban bankin ya fito da su, bai yi tuya ya manta da albasa ba, domin bai yi watsi da yadda wasu mutane, wadanda su suka fi yawa cikin al’umma ba, ba su damar ci gaba da hada-hadar kasuwanci kamar yadda suka saba.

Daidaito
Sabo Ahmad
+ postsBio
  • Sabo Ahmad
    https://hausa.leadership.ng/author/sabo-ahmad/
    An Gurfanar Da Mutum 3 Bisa Laifin Lakada Wa Wani Duka Har Lahira
  • Sabo Ahmad
    https://hausa.leadership.ng/author/sabo-ahmad/
    Dalilin Da Ya Sa Kotu Ta Tasa Keyar Dakta Idris Dutsen Tanshi Zuwa Gidan Yari
  • Sabo Ahmad
    https://hausa.leadership.ng/author/sabo-ahmad/
    Uwa Ta Mutu A Kokarin Raba Fada Tsakanin ‘Ya’yanta A Abuja
  • Sabo Ahmad
    https://hausa.leadership.ng/author/sabo-ahmad/
    ’Yan Fashi Sun Yi Shigar Injiniyoyi, Sun Saci Manyan Na’urorin Sadarwa

MASU ALAKA

Yadda Na Sayar Da Kadarori Na Don Ɗaukar Nauyin Ɗalibai A Ƙasashen Waje – Kwankwaso
Manyan Labarai

Zargin Ɓata Suna: Kwankwaso Ya Yi Barazanar Neman Diyyar Naira Biliyan 10 Kan Wani Malamin Coci

June 24, 2026
Tinubu Ya Gaza Wajen Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya — Atiku
Manyan Labarai

Atiku Ya Soki Tsare El-Rufai, Ya Ce Sharuɗan Belinsa Sun Yi Tsauri

June 24, 2026
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Kama Wani Mutum da Harsasai 174 A Nasarawa

June 24, 2026
Next Post
Me Ya Sa Karin Kamfanonin Ketare Suka Samu Ra’ayin Bai Daya Kan Zuwa Kasar Sin Don Raya Kansu?

Me Ya Sa Karin Kamfanonin Ketare Suka Samu Ra’ayin Bai Daya Kan Zuwa Kasar Sin Don Raya Kansu?

LABARAI MASU NASABA

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

June 24, 2026
’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

June 24, 2026
Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

June 24, 2026
Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

June 24, 2026
Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

June 24, 2026
Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

June 24, 2026
Sabbin Ministoci

Kafa ‘Yansandan Jihohi: Majalisa Ta Amince Da Tsarin ‘Yar Tinƙe Wajen Kaɗa Ƙuri’a 

June 24, 2026
Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

June 24, 2026
Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

June 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.