Rahotanni daga kamfanin kula da makamashi na kasar Sin na cewa, babban aikin “Samar da wutar lantarki daga hasken rana a wajen da ake kiwon kifi” na kasar Sin, wato tashar samar da lantarki daga hasken rana mai karfin kilowatt miliyan 1.09 dake gabar teku a lardin Hebei, wadda kamfanin zuba jari kan makamashi na Guohua ya gudanar, ta riga ta fara aiki cikin nasara.
Hada kiwon kifi da aikin samar da lantarkin na nufin an girke na’urorin tattara haske a cikin ruwan da ake kiwon kifi. Wato na’urorin na sama, yayin da ake kiwon kifi a kasansu.
- An Yi Bikin Nuna Fina-Finai Da Shirye-Shiryen Telabijin Na Habasha Da Sin
- Yadda Hukumar Leken Asirin Burtaniya Ta Dakile Yunkurin Kisan Fafaroma
Tashar tana cikin birnin Cangzhou na lardin Hebei, a bakin tekun Bohai, kuma ta kunshi jimillar na’urorin samar da lantarki daga hasken rana guda miliyan 2.31. Aikin ya dogara ne da albarkatun kasa na musamman da kuma masana’antar kiwon kifayen teku ta Cangzhou, don aiwatar da binciken muhimman fasahohi da aikace-aikace kan “samar da wutar lantarki daga hasken rana a wajen da ake kiwon kifi” ba tare da gurbata muhalli ba, da kuma binciken sabuwar hanyar bunkasa masana’antar hada makamashi da kiwon kifaye.
A cewar babban jami’in dake kamfanin kula da makamashi na kasar Sin, bayan tashar ta fara aiki, yawan wutar lantarkin da za ta samar a kowace shekara zai kai kusan kWh biliyan 1.86, wanda zai kai kusan adadin wutar lantarkin da mazauna miliyan 2.79 ke bukatar a duk shekara. Haka kuma yana iya tsimin gawayi kusan tan dubu 561 da kuma rage fitar hayakin carbon dioxide kusan tan miliyan 1.4 a kowace shekara. Ban da hakan, aikin zai iya taimakawa wajen gina sabon tsarin samar da wutar lantarki ta makamashi mai dorewa a wurin, wanda zai kawo babban alheri a fannonin tattalin arziki da muhallin hallitu da kuma zamantakewar al’umma. (Safiyah Ma)