Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana rage kuɗin ruwa, daga kashi 27.5 zuwa kashi 27.
Gwamnan Babban Bankin, Olayemi Cardoso ne ya bayyana haka, a ranar Litinin jim kaɗan bayan kammala taron Kwamitin Ƙwararrun Bada Shawarwari kan Tattalin Arziki (MPC), a Abuja.
Cardoso ya ce kwamitin ya amince a rage kuɗin ruwa da ɗigo .50, wato daga kashi 27.5 bisa 100, ya koma kashi 27 bisa 100.
Wannan ne dai karo na farko da adadin gejin kuɗin ruwa ya yi ƙasa, wato mafi ƙaranci a cikin shekaru biyar.
Gwamnan na CBN ya ce an yanke shawarar rage kuɗin ruwan ne domin ci gaba da bunkasuwar tattalin arzikin cikin gida (GDP), da karyewar hauhawar farashi, wanda tsawon watanni biyar kenan ana samu a jere.
Tuni, dama masana suka yi hasashen cewa malejin tsadar rayuwa zai ƙara yin ƙasa sosai a sauran watannin ƙarshen 2025.
Haka kuma wani dalilin rage kuɗin ruwan shi ne domin a ci gaba da ƙarfafa tattalin arziki.