Shugaban hafsan sojin kasa (COAS), Laftanar-Janar. Olufemi Oluyede, ya kalubalanci sabbin jami’an rundunar sojin da aka yaye a makarantar horon soji da ke Zaria, jihar Kaduna da su kasance cikin shiri domin yaki da ta’addanci da tada kayar baya a kasar.
Janar Oluyede ya yi wannan batu ne a wurin bikin yaye jami’ai 6,195 na shekarar horo ta 88 da aka dauka a ranar Asabar, yayin da ya jaddada mahimmancin jajircewa, kwarewa da juriya a cikin mawuyacin hali.
- ‘Yan Wasa Biyar Da Suka Taka Rawar Gani A Kofin Zakarun Turai
- Wakilin Sin A IAEA Ya Yi Tir Da Harin Isra’ila Kan Cibiyoyin Sarrafa Nukiliyar Iran
Ya kuma jaddada muhimmancin tabbatar da martabar sojojin Nijeriya, sannan ya tunatar da wadanda aka yaye cewa, rayuwar soja ta sadaukarwa ce da kishin kasa, inda ya kara da cewa; “Rundunar Sojin Nijeriya kwararriyar cibiya ce da aka dora wa alhakin tabbatar da ‘yancin kasarmu mai girma Nijeriya.
“Yayin da kuka fita a yau kuma kuka samu matsayinku a wannan ma’aikata mai daraja, ku sani cewa za ku zama wani bangare na hanyoyin magance kalubalen ta’addanci da ‘yan tada kayar baya acikin al’ummarmu, don haka duk inda aka tura ku, tilas ne ku aiwatar da abinda aka horar da ku, kuma ku nuna jajircewa wajen fuskantar matsaloli.
“Tafiyar mil dubu tana farawa ne da taku daya, don haka, tafiyarku ta fara ne a ranar 13 ga watan Janairun 2025, lokacin da kuka fara amsar horo na aikin soji, an shirya muku duk wani abu da za ku iya fuskanta na kalubale, kuma ina mai tabbatar muku da cewa, za ku fuskanci kalubalen da da farko zaku ga kamar ba za a iya shawo kansu ba. Amma kuna jajircewa, sai su zama tarihi”. In ji shi
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp