Babban Hafsan Sojin kasa (COAS), Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya nemi sojojin Nijeriya da su rubanya kokarinsu na yi wa kasa hidima musamman a yaki da rashin tsaro.
Ya amince cewa, sojojin suna aiki cikin “mawuyacin yanayi mai matukar kalubale” amma akwai bukatar kara jajircewar.
- An Kaddamar Taron Tattaunawa Game Da Raya Bangaren Al’adun Sin
- Lookman Ya Zura Kwallo Uku Rigis Yayin Da Atalanta Ta Lashe Kofin Europa League
Lagbaja ya yi wannan kiran ne a ranar Alhamis yayin da yake jawabi ga sojojin yayin ziyarar aiki da ya kai a runduna ta 35 da ke Barikin Alamala, Abeokuta, a Jihar Ogun.
Lagbaja ya tabbatar wa dakarun cewa, hedikwatar rundunar tsaro ta kasa, ta himmatu wajen shawo kan kalubalen da sojojin ke fuskanta cikin gaggawa.