Babban Mai Shara’a na Kasa, Justice Olukayode Ariwoola ya gargadi alkalan da aka ware domin jin korafe-korafen zaben 2023 su gudanar da gaskiya da amana wajen zantar da hukunci a kasa kar su kuskura su ci amanan ‘yan Nijeriya a 2023.
Babban mai shari’a na kasa ya bayyana hakan ne a lokacin bude taron bita na kwanaki hadu da aka shirya wa alkalan da za su saurari korafe-korafen zabe a cibiyar shari’a ta kasa da ke Abuja a ranar Litinin da ta gabata.
Justice Ariwoola ya bukaci jami’an da ke sashin shari’a da su cire duk wata son zuciya wajen gudanar da harkokin shari’a a lokacin da suke yanke hukunci kan a kotuna.
“Ya kamata alkalai su zama masu gaskiya da rukon amana a lokacin da suke zantar da hukunci kan wadanda suka tsaya takara a mukamai daban-daban a zaben 2023, domin su ne masu kwato wa wadanda ba a yi musu adalci ba hakkinsu, sannan ya zama wajibi su yi kokarin sauke nauyin da Allah ya daura musu cikin gaskiya da rikon amana.
“Ba a bukatar jami’an da ke sashin shari’a su kasance masu rashin gaskiya wajen gudanar da ayyukansu da ka daura musu, ina mai tabbatar muku da cewa al’umma suna da matukar kwarin gwiwa a kanku wajen yi musu adalci lokacin sauraran karar zabe.
“Gaskiya nauyi ne da ya rataya a wuyanku lokacin da kuke gudanar da ayyukanku na alkalanci, saboda ku kuke amso wa mara karfi hakkinsa ta hanyar gaskiya.
“Dole ku tashi tsaye wajen yakar son zuciya a wurin gudanar da ayyukanku na alkalanci, musamman wajen sauraren korafe-korafen zabe,” in ji shi.
Haka ita ma shugaban kotun daukaka kara, Justice Monica Dongban-Mensem ta bayyana cewa alkalan guda 277 wadanda aka zabe domin sauraron korafe-korafen zabe wadanda suka hada da na babban kotun tarayya 4 da kotun sauraron karar ma’aikata ta kasa 3 da na babban kotun Abuja da na jihohi 213 da kotun gargajiya 13 da kotun shari’ar Musulunci 27 da kuma kotun majastiri 17.
Ta bukaci alkalan da su yi kokarin gudanar da aiki bisa kwarewarsu wajen sauke nauyin da aka daura musu.
Mun Shigar Da Kara 600 Kan Laifuka Gabanin Zabe – INEC
A nasa jawabin, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa a yanzu haka hukumarsa ta shigar da kara 600 daga zaben fid da gwani na jam’iyyun siyasa daban-daban da suka gudanar domin shiga zaben 2023.
Ya kara da cewa hukumarsa ta yi nazarin kan hukunce-hukuncen zaben 2019, musamman wadanda suke kewaye da zabukan gwamnoni da zabukan cike gurbi da aka kammala a wasu yankun wadanda suke bukatar kai kara.
“Cikin makonni biyu da suka gabata, jam’iyya daya kacal mun samu korafi har guda 70 wadanda muka shigar a kotu a cikin mako daya da ke neman amincewa ko sauya ‘yan takara bayan wa’adin da muka saka kan jaddawalin zaben 2023 ya kare.
“An dai kai wasu korafe-korafen zuwa kotun koli,” in ji shi.
Ya zayyano yadda aka samu nasarori a cikin dokar zaben 2022 wanda aka inganta babban zaben 2023, musamman ma samar da na’urorin bayyana sakamakon zabe da hukumar zabe za ta samu nasarar cike gibi a tsakanin dokar zaben 2010.
“Haka kuma, sabon dokar zabe ta bayar da damar shigar da hurimin sauraron kararrakin korafe-korafin gabanin zabe a babban kotun tarayya kan zaben ‘yan takara domin a rage cinkoson a bangaren doka da kuma yin amfani da kotuna ba bisa ka’ida ba wajen yanke hukuncin kan hurumin da kotuna suke da shi,” in ji shi.