Bangaren majalisar dokoki na daya daga cikin manyan fulogan gwamnati uku a tsarin shugabancin Nijeriya, shi ya sa ‘Yan Nijeriya da dama kan dora alamar tambaya game da wasu abubuwa da ke faruwa a kasa a kan majalisa.
Ganin yanayin da ake ciki a kasar nan a halin yanzu, sanata mai wakiltar mazabar Katsina ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, SANATA ABDULLAHI KABIR BARKIYA ya tattauna da NANA KHADIJA‘ YARZURU inda ya warware zare da abawa kan kalubalen da majalisa ke fuskanta da kuma wasu al’amura da suka shafi kasa da mazabarsa. Ga tattaunawar kamar haka:
- Tinubu Ga Peter Obi: Ka Gargaɗi Magoya Bayanka Kan Ɓata Min Suna
- Yunkurin Tsige Shugaba Buhari Abin Takaici Ne Matuka —Abdullahi Adamu
Da farko, ya mai girma Sanata, masu kallo da sauraro za su so su ji ko wane ne mai girma Sanata Abdullahi Kabir Barkiya a takaice?
Sunana Sanata Abdullahi Kabir Barkiya an haife ni a garin Barkiya cikin karamar Hukumar Kufi dake Jihar Katsina, na kuma yi makaranta a nan karamar Hukumar Kurfi, cikin garin Kurfi ana ce mata Kurfi Primary School, na yi makarantar Gobernment Secondary Technical School, daga na sai na wuce Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, na yi makaranta ta share fagen shiga jami’a shekara daya. Daga nan kuma sai na samu gurbin karatu inda na yi Digiri akan ‘Cibil Engineering’, wanda yake shekara uku na yi, daga nan na tafi bauta wa kasa (NYSC) a wancan lokacin a Jihar Gongola wanda a yanzu Jihar Adamawa kenan.
Da na kare Allah da ikonsa a lokacin aiki ba ya wahala, idan ma mutum ya karanta fannin Injiniya ko likitanci, akanta da dai sauransu zai samu aikin yi, to shi ne na samu aiki a lokacin a wurare uku Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje suka dauke ni, sai kuma Cibil Serbice Commission suma sun dauke ni, sai kuma ofishin JAMB, a lokacin Jihar Kaduna ce ba a yi Jihar Katsina ba, suka dauke a Ma’aikatar Gidaje, sai kuma NNPC ma sun dauke ni.
To cikin lamarin Allah da ikonsa ina cikin wannan aiki har na kai mataki na 17 na kai matsayin Darakta na ayyuka, daga nan kuma na zo (SEMA) na yi shekara biyu ina Darakta, kuma na yi shekara biyu ina Manajan Darakta a wannan hukuma ta gyaran hanyoyi.
Bayan haka kuma, na fara wadannan ayyuka na fadada hanya daga Legas zuwa Ibadan zuwa Shagamu, to tun da na fara wadannan ayyukan daga nan ne kuma Allah da ikonsa tun da an ce komai kaddara ce, na yi murabus daga wannan aikin saboda radin kaina na zo na shiga siyasa. To a lokacin da na shiga siyasa na shiga jam’iyyar PDP na yi takarar gwamna da ban yi nasara ba na dawo APC na yi takarar Sanata, wanda kuma har yanzu ina nan a matsayin Sanata in sha Allahu.
To za mu so mu ji ko me ya jawo ra’ayinka kan harkar siyasa?
To abin da ya ja hankalina na shiga siyasa yana da yawa, na farko dai duk aikin da nake yi ina amfana ne ni da iyalina, amma yanzu da na fito siyasa idan Allah ya sa na kai gaci zan taimaka wa jama’a wajen samun aikin yi da kuma ba da tallafi na karfafa wa mata da maza domin su dogara da kansu, to wannan dai shi ne a takaice abin ya ja hankalina zuwa shiga siyasa.
Masha Allah, to dangane da yanayin matsin rayuwa da ake ciki, shin akwai wani kudiri da majalisa ke kokarin gabatarwa domin ganin an samu sauki?
To Alhamdulillahi, kullum majalisa takan yi kokarin ganin ta kawo hanyoyin da take ganin an samu sauki, ko ni kaina na yi kokarin gabatar da hakan wajen kira ga gwamnatin tarayya ta hanyar kawo wata doka da za ta sa a kafa wata hukuma da za ta tallafa wa talakawa domin al’umma su samu sauki, amma da an kafa ba ta zuwa ko ina, to akwai kudirori irin wadannan da yawa. Kamar misali akwai kudiri da na kawo na ce a canja doka ta kananan hukumomi na ainihi ta yadda za a fadada ta yadda za a rika daukar ma’aikata da yawa, amma da muka je sai ministocin suka rika ganin kamar ana so a rage musu wani karfi ne, to duk irin wadannan matsalolin ne muke fama da su.
Amma yanzu babbar matsalarmu ita ce tsaro, wacce tun lokacin Jonathan, tun lokacin ma Umaru Musa ‘Yar Adua aka fara da Boko Haram na wajejen Maiduguri, to aka taho dai har zuwa yanzu matsalar tana nan.
To kuma matsalar na nan Arewacin Nijeriya, Katsina, Sokoto, Zamfara, da Kaduna kuma masu garkuwa da mutane, a sace mutane su ce sai an ba su kudi, in ba’a ba su kudi ba su kashe mutane. Har yanzu matsalar da take ci mana tuwo a kwarya ita ce ta rashin tsaron nan. Muna ta rokon Allah ya kawo mana karshen wannan lamari.
Komai a rayuwa akan samu nasara kuma akan fuskanci kalubale, shin ko za ka bayyana mana irin kalubalen da majalisa ke fuskanta a halin yanzu?
To Alhamdu lillahi, babban kalubalen majalisa shi ne za a zauna a gabatar da kudiri amma ba za a aiwatar ba, misali an zauna an yi doka na wani abu da zai amfani al’umma sai kuma abin ya wuce ba tare da an tabbatar da shi ba, to wannan ita ce babbar matsalar da muke fama da ita. Sai kuma abin da ya shafi kudi.
Sannan akwai abubuwan da suke hana ruwa gudu abin da ba dadi, ta yadda za ka ga ana so a yi abin da zai kai ga talakawa amma wasu ba sa son hakan, su ma wadannan suna daga cikin matsalolin da muke ta fama da su.
To ko za ka yi wa masu kallo bayani kan romon Dimukradiyyar da ka shayar da al’ummar da kake wakilta?
Alhamdulillahi, lokacin da na zo a yakin neman zabe na yi bayanin cewa zan tallafa wa mutane, kuma na bayar da tallafin kudade ga mata masu kananan sana’o’i, kuma an ga yadda muka ba da tallafi ga matasa domin su samu aikin yi, mun bayar da horo yadda aka koya wa matasa yadda ake yin na’ura mai ba da hasken wutar lantarki ta hanyar haske rana wato (Solar), da koyar da aikin gyaran wutar lantarki, da koyon aikin gyaran mota, duk an gani mun yi. Sannan akwai lokacin da muka samu labarin makarantun da yara ke karatu babu littattafai babu abin zama duk muka yi kokari aka samar da su.
Kuma akwai lokacin da na ba da tallafin Babura, kekunan dinki, injinan ban ruwa wajen amfani a noman rani, to duk mun yi wadannan abubuwa. Kuma Allah ya taimake mu mun sama wa yara aiki a hukumar ‘yan sanda, Hukumar Kiyaye Hadura FRSC, akwai abubuwa da na yi, kin ga a fannin nom ana ba da tallafin taki Hukumar Kula da Shige da Fice Ta kasa da dai sauran wurare da dama duk mun yi kokarin ganin mun sama wa matasa aikin yi domin su tsaya da kafarsu. Na yi abubuwa da dama na ci gaban jama’a kadanda jama’a suka amfana sosai.
A karshe za mu ka dan ba da wasu shawarwari domin gina rayuwa ta gobe?
To Alhamdulillahi shawarar da zan bayar ita ce mu ci gaba da yi wa wannan kasa addu’a domin samun zaman lafiya, sannan kuma mu ci gaba da hakuri wannan hali na kuncin rayuwa, in Allah ya so komai zai wuce, in muka ci gaba da hakan za mu samu saukin rayuwa.