A yayin da ranar 29 ga watan Mayu ke kara karatowa, ranar da za a rantsar da shugaban tarayyar Nijeriya da sauran zababbun gwamnoni a fadin tarayya kasa, Babban sufeton ‘yansanda Nijeriya IGP Usman Baba ya ja kunnen ‘yan siyasa da sauran masu barazanar kawo wa ranar dimokradiyyar kasa cikas.
Babban sufeton ya yi wannan gargadi ne a taron manema labarai da ya kira a ofishinsa da ke Abuja, ya ce, rundunar ‘yansanda ba za su zura ido ba ana yi wa shirin kaddamar da da sabuwar gwamnati barazana.
- Shugaban Tsimi Da Tanadi Ya Warware Mishkilar Dimbin Bashin Da Ake Bin Jihar Kaduna
- Da Dumi-dumi: ‘Yansanda Sun Tabbatar Da Yin Garkuwa Da ‘Yan Hidimar Kasa A Jihar Ribas
Ya ce,, “Ba za a iya kiyasta bukata da muhimmancin zaman lafiya a rayuwar mu ta yau da kullum a Nijeriya ba, musamman bukatar tabbatar da tsaro a daidai wannan lokaci na rayuwar kasar mu Nijerriya, a saboda haka rundunar ‘yansanda na aiki tare da dukkan jami’an tsaro a Nijeriya, za kuma mu ci gaba da sanya ido a kan tsirarun ‘yansiyasa masu shirin tayar da fitina a kan haka muke kira gare su da su shiga taitayinsu, don ba za a lamunce musu ba..
“Da farko, rundunar ‘yansandan Nijeriya na gargadi ga dukkan ‘yan siyasa masu son tayar da zaune tsaye da masu goya musu baya, musamman ‘yan bangan su da suke turawa gaba-gaba da su gaggauta janye mugun shirinsu, su kuma sani cewa, furuce-furucen su na tayar da hankulan al’umma adai-dai lokacin da ake shirye-shiryen bukukuwan mika mulki ga sabuwar gwamnati a ranar 29 ga watan Mayu 2023.
“Na biyu kuma duk wani mahaluki ba tare da nuna banbancin a wacce jam’iyyar siyasa ko kungiya yake da ya ci gaba da harkokin da za su iya kawo cikas ga shirin ranstar da sabuwar gwamnati ko kuma barazana ga zaman lafiyar al’umma, tabbas rundunar ‘yansanda za su dakile shi ba tare da saurarawa ba, don kuwa mun shirya aiki da dukkan rundunonin tsaro wajen tabbatar da shirin rantsar da sabuwar gamnati bai samu wata matsala ba.
“Na uku, ya kamata al’umma su fahimci cewa, rantsar da sabuwar gwamnati a dukkan mataki abu ne da ya shafi kundin tsasrin mulkin Nijeriya, a kan haka rundunar ‘yansanda na da hakkin ganin ta kare duk wani abin da ke tare da tsarin mulkin Nijeriya, za kuma mu tabbatar da kare tsarin mulkin Nijeriya kamar yadda muka yi rantsuwar haka tun a farkon kama aikimu.
“A kan haka nike sanar da al’umam Nijeriya cewa, muna nan a kan shirin mu na kare dukkan kundin tsarin mulkin Nijeriya ba tare da ja da baya ba.. Za mu kare dimokradiyya a dukkan mataki. Za mu tabbatar da an kare ranar 29 ga watan Mayu, ranar da za a rantsar da shugaban tayayyar Nijeriya da sauran wadanda za a rantsar a fadin Nijeriya a cikin kwanciyar hankali kamar yadda aka shirya.”
Ya kuma bukaci al’umma kasashen duniya su kaucewa dukkan ayyukan da zai iya haifar da barazana ga wannan rana ta hanyar yin wasu furuce-furice a kafafen sadarwa na zaman ida za su iya harfar da tashin hankali.