Babban titin mota na birnin Nairobin kasar Kenya, wanda wani kamfanin kasar Sin ya gina ya samu lambar yabo ta AMTA. Titin mai tsawon kilomita 27.1, ya samu lambar ne a jiya Juma’a, yayin biki karo na 3, na “Africa Mashariki Transport Award ko (AMTA), bisa yadda ya zamo mai kunshe da fasahohin zamani marasa gurbata yanayi, da ba da damar zirga zirga ba tare da tangarda ba a Kenya, da ma sauran kasashen yankin gabashin Afirka.
An fara gudanar da bikin ba da lambar yabo ta Afirka ko AMTA ne tun daga shekarar 2022, domin karrama fasahohin raya sufuri a sassan kasar Kenya, da ma sauran yankunan dake kewaye da kasar.
- Shugaba Xi Ya Gana Da Kantoman Yankin Musamman Na Macao Na Kasar Sin
- Kakakin Ma’aikatar Tsaron Sin Ya Yi Tir Da Sayar Da Makamai Da Amurka Ke Yi Wa Taiwan
A watan Satumban shekarar 2020 ne aka fara gudanar da aikin ginin babbar hanyar mota ta Nairobi, kana aka kaddamar da ita a hukumance a watan Yulin 2022, bayan fara gwajin ingancin ta tun daga watan Mayun shekarar.
Kaza lika, tun bayan kaddamar da amfani da titin, ya taimaka matuka wajen rage tsayin tafiya zuwa yankunan kudancin birnin Nairobi, inda babban filin jirgin saman kasar yake, da yankunan wajen birnin Westlands, daga tafiyar sa’o’i 2 a lokacin yawan zirga zirga zuwa mintuna 20 kacal. (Saminu Alhassan)