Allah Ya yi wa yayan tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, Alhaji Suleiman Sambo, rasuwa a ranar Litinin bayan fama da rashin lafiya.
Marigayi Alhaji Suleiman Sambo, ya rasu yana da shekaru 82 duniya, kuma tuni aka yi jana’izarsa.
- Tinubu Ya Taya Trump Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Amurka
- Xi Ya Bukaci A Kara Zage Damtse Wajen Farfado Da Kauyuka
Cikin gajeriyar nasihar da ya gabatar yayin jana’izar, babban limamin masallacin kwalejin kimiyya da fasaha ta Kaduna, Uztaz Sadiq Yusuf, ya gargadi al’ummar Musulmi da su mayar da hankali wajen bautar Allah.
Ya yi nuni da irin gudunmawar da marigayin ya bayar a lokacin da yake raye.
Marigayi Alhaji Suleiman Sambo, ya yi aiki a ma’aikatar buga takardu ta gwamnati ƙarƙashin tsohuwar ma’aikatar yaɗa labarai da harkokin cikin gida ta jihar Kaduna.
Ya yi ritaya a matsayin babban Sufeto a 1994 bayan kwashe shekaru 35 cikin aikin.