A rana Juma’a da ta gabata, aka kaddamar da gasar wasannin kankara ta nahiyar Asiya karo na 9, a birnin Harbin na lardin Heilongjiang na kasar Sin. Wannan gasa ta kasance babbar gasar wasannin kankara ta kasa da kasa karo na 2 da Sin ta karbi bakuncinta, biyo bayan gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi da ta gudana a birnin Beijing na Sin, a shekarar 2022. An ce, gasar wasannin kankara ta wannan karo ta samu halartar ‘yan wasa fiye da 1270 da suka zo daga kasashe da yankuna 34 dake nahiyar Asiya, alkaluman da suka kai matsayin koli a tarihi. Inda har wasu kasashen da ba sa samun yanayi mai sanyi da muhalli mai kankara a cikin gida, kamarsu UAE, da Vietnam, da Indonesia, da Thailand, da dai sauransu, su ma suka tura tawagogi su halarci gasar.
Wata babbar ma’ana ta gasar ta wannan karo, ita ce tabbatar da hadin kan kasashen nahiyar Asiya. Ko da yake tattalin arzikin nahiyar na ta samun ci gaba cikin matukar sauri cikin shekaru 50 da suka gabata, sauyawar yanayin al’amuran siyasa na duniya, da takarar da ake yi tsakanin kasashe daban daban, suna ci gaba da haifar da kalubale a nahiyar. Bisa la’akari da wannan yanayin da ake ciki, taken gasar wasannin kankara ta nahiyar Asiya ta wannan karo na “tabbatar da hadin kan kasashen nahiyar Asiya” ya nuna bukatar dake akwai, gami da burin jama’ar kasashen Asiya na karfafa zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki a kasashensu.
A wajen bikin kaddamar da gasar wasannin kankara ta wannan karo, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarwarin karfafa niyyar tabbatar da zaman lafiya, da ci gaban tattalin arziki, da cudanya, da kauna, tsakanin kasashen Asiya, gami da kasashen duk duniya baki daya, wadanda suka nuna yadda kasar Sin ke kokarin sauke nauyin dake wuyanta, na nemo wa duniya hanyar samun ci gaba mai dacewa, a matsayinta na wata babbar kasa. (Bello Wang)