• English
  • Business News
Monday, November 3, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Babbar Kasa Ita Ce Ke Dinke Baraka Ba Kawo Rarrabuwar Kawuna Ba

by CMG Hausa
3 years ago
Kasa

Yayin taron Shangri-La, da ministocin tsaron kasashen yankin Asiya ke muhawara kan muhimman kalubalen tsaro da yankin ke fuskanta tare da gabatar da dabarun shawo kansu, sakataren tsaron Amurka Lloyd J. Austin III ya tabo wasu batutuwa da suka shafi kasar Sin.

Ya ce a baya-bayan nan, ana samun matsi daga rundunar sojin kasar Sin a yankin tekun kudancin kasar. Sai dai rahotanni sun nuna cewa, sama da jiragen ruwa 100,000 ne ke zirga-zirga a tekun a kowacce shekara, kuma babu wanda ya taba fuskantar barazana.

  • Sin Ta Gudanar Da Ayyukan Nazarin Kayan Tarihi Fiye Da 8800 A Cikin Shekaru 10 Da Suka Gabata

Tabbas kasar Sin ba ta takalar fada, sai dai mayar da martani idan aka takale ta. Don haka, duk wani wanda zai yi korafi game da fuskantar barazana daga rundunar sojin kasar Sin, to takalarta ya yi ko keta dokokin, domin Sin ba ta daukar wargi.

Ya kara da cewa, ba su sauya matsayarsu kan manufar kasar Sin daya tak a duniya da yarjejeniyoyin da kasashen biyu suka cimma ba, amma kuma za su ci gaba da taimakawa Taiwan zama mai dogaro da kanta a fannin tsaron kai.

Shin me hakan ke nufi? Duk wanda ya amince da ka’idar kasancewar kasar Sin daya tak da gaske, ya san cewa bai halarta ya yi wata hulda ta kai tsaye da yankin Taiwan ba.

LABARAI MASU NASABA

Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai

Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka

Ikirarin taimakawa Taiwan ta fuskar tsaro, ya nuna karara cewa, Amurka na goyon bayan masu neman ballewar yankin, abun da Sin ta sha nanata cewa ba mai yuwuwa ba ne. Kuma a matsayinta na mai wakiltar baki daya Jamhuriyar kasar Sin, batun tsaron Taiwan, hakki ne na kasar Sin, ba wata kasar waje ba.

Amurka na ikirarin ta damu da tsaron yankin Asiya. Idan har da gaske take, ganin cewa dukkan kasashen yankin na da cikakken iko da yankunansu, kamata ya yi a yi la’akari da bukatun da damuwar kowacce kasa.

Kamata ya yi a girmama ’yancin kasashen yankin da hanyoyin ci gaba ko tafiyar da mulki ko na tabbatar da tsaro da suka zabarwa kansu. Bai dace wata kasa ta yi kokarin kakkaba tsarinta a kan wata ba, domin mai daki shi ya san inda yake masa yoyo.

Har ila yau, ya ce matsayin babbar kasa na nufin daukar babbar nauyi. Sai dai sam wannan suna ba ta dace da Amurka ba. Babbar kasa ita ta san ya kamata, ita ke dinke baraka idan ta bullo, ba rura wutar rikici ba, ita ke hade kan al’umma ba kawo rarrabuwar kawuna ba. (Fa’iza Mustapha)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai
Daga Birnin Sin

Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai

November 3, 2025
Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka
Daga Birnin Sin

Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka

November 3, 2025
Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan

November 3, 2025
Next Post
Yang Jiechi Ya Gana Da Mai Taimakawa Shugaban Amurka Kan Harkokin Tsaron Kasa

Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya

Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya

November 3, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki

Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki

November 3, 2025
Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro

Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro

November 3, 2025
Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan

November 3, 2025
Kwamishinan Ƴansanda Na Kano Ya Karrama Sabbin Jami’an Da Aka Ƙara Wa Matsayi

Kwamishinan Ƴansanda Na Kano Ya Karrama Sabbin Jami’an Da Aka Ƙara Wa Matsayi

November 3, 2025
Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 19, Sun Ƙwato Makamai A Kano

Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 19, Sun Ƙwato Makamai A Kano

November 3, 2025
Zamfara Ta Tashi Daga Matsayi Na 36 Zuwa Na 17 A Shekara Biyu Ƙarƙashin Gwamna Lawal — Rahoton BudgIT

Zamfara Ta Tashi Daga Matsayi Na 36 Zuwa Na 17 A Shekara Biyu Ƙarƙashin Gwamna Lawal — Rahoton BudgIT

November 3, 2025
Sabon Muƙaddashin Shugaban PDP Ya Sha Alwashin Maido Da Martabar Jam’iyyar Kafin 2027

Sabon Muƙaddashin Shugaban PDP Ya Sha Alwashin Maido Da Martabar Jam’iyyar Kafin 2027

November 3, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.