• English
  • Business News
Thursday, October 30, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Babbar Magana

by CMG Hausa
3 years ago
SIN

Fari, da ambaliyar ruwa, kwararar hamada, yanayi na sanyi da zafi da suka wuce kima da makamantansu, na daga cikin matsalolin da sauyin yanayi ke haddasawa, wadanda kuma ke ci gaba da addabar bil-adama. Bayanai na nuna cewa, kasashen dake yankin kahon Afirka na daga cikin wadanda ke fama da wannan matsala.

Sakamakon matsalar fari da yankin kahon Afirka ke fuskanta, ya sa asusun tallafawa kananan yara na MDD ko UNICEF a takaice, ya kaddamar da asusun gaggawa, inda yake neman taimakon dalar Amurka biliyan daya, domin tallafawa yaran dake rayuwa a sassan yankin kahon Afirka a shekarar 2023 dake tafe.

  • Amurka Na Ci Gaba Da Cin Kare Ba Babaka A Kasar Syria

UNICEF ya ce, ya sake nazartar kudaden tallafin gaggawa na jin kai da ake bukata, domin kare rayuwar yara dake kasashen Habasha, da Kenya da Somaliya, inda adadin kudaden da ake bukata domin gudanar da ayyuka ya sauya, daga dala miliyan 879 a watan Satumba zuwa dala biliyan daya a shekara mai zuwa. Babbar magana wai Dan-sanda ya ga gawar soja.

Wannan na zuwa ne, bayan asusun da aka kaddamar a taron sauyin yanayi na kasar Masar, duk da nufin magance illar da wannan matsala ta sauyin yanayi ke haifarwa duniyar bil-Adama da abubuwan dake rayuwa a cikinta.

Bayanai na nuna cewa, yaran dake yankin kahon Afirka na fuskantar mawuyacin hali na rayuwa, sakamakon mummunan fari da aka jima ba a ga irin sa ba a tarihin kasashen 3, baya ga tashe-tashen hankula dake ci gaba da addabar arewacin Habasha. Don haka, taimakawa wannan rukuni na al’umma dake zama manyan gobe, zai taimaka ga ci gaban al’ummar yankin ne baki daya.

LABARAI MASU NASABA

Sin Za Ta Harba Kumbon Shenzhou-21

Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai

Masharhanta na cewa, mummunan tasirin sauyin yanayi na barazana ga rayukan yara, abin da ya sanya asusun mayar da hankali, ga dabarun jurewa da iya rayuwa tare da tasirin sauyin yanayi, a matsayin muhimman bangarorin tallafin jin kai da yake aiwatarwa. Kuma hakan zai taimaka matuka, wajen kaiwa ga yaran dake rayuwa cikin yanayin tashe-tashen hankula, tare da ba da damar taimaka musu, da al’ummun su shiryawa abubuwan daka iya aukuwa a nan gaba. Rigakafi aka ce ya fi magani. Fata dai shi ne, kudaden da za a tara za su kai ga wadanda aka yi dominsu. Domin ka da a fake da guzuma ana harbin karsana. (Ibrahim Yaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin Za Ta Harba Kumbon Shenzhou-21
Daga Birnin Sin

Sin Za Ta Harba Kumbon Shenzhou-21

October 30, 2025
Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai
Daga Birnin Sin

Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai

October 30, 2025
Sakamakon Nazarin CGTN Ya Yabawa Gudunmuwar Sin Ga Dunkulewar Yankin Asiya Da Pasifik
Daga Birnin Sin

Sakamakon Nazarin CGTN Ya Yabawa Gudunmuwar Sin Ga Dunkulewar Yankin Asiya Da Pasifik

October 29, 2025
Next Post
Rashin Amincewa Da Daidaita Tsarin Rigakafi Da Shawo Kan Cutar COVID-19 Na Sin Ya Saba Gaskiya

Rashin Amincewa Da Daidaita Tsarin Rigakafi Da Shawo Kan Cutar COVID-19 Na Sin Ya Saba Gaskiya

LABARAI MASU NASABA

Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda 

Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda 

October 30, 2025
Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC

Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC

October 30, 2025
Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai

Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai

October 30, 2025
Wata 3 Da Naɗin Shugaban APC, Sunan Yilwatda Har Yanzu Na Nan A Matsayin Minista A Shafin Ma’aikatar

Wata 3 Da Naɗin Shugaban APC, Sunan Yilwatda Har Yanzu Na Nan A Matsayin Minista A Shafin Ma’aikatar

October 30, 2025
Tinubu Ya Nada Musa Aliyu A Matsayin Shugaban ICPC

Tinubu Ya Amince Da Ƙara Harajin Shigo Da Man Fetur Da Dizal Zuwa Kashi 15

October 30, 2025
Sin Za Ta Harba Kumbon Shenzhou-21

Sin Za Ta Harba Kumbon Shenzhou-21

October 30, 2025
Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai

Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai

October 30, 2025
Sojoji Sun Ceto Wani Mutum Da Aka Sace A Taraba

Sojoji Sun Ceto Wani Mutum Da Aka Sace A Taraba

October 30, 2025
Majalisar Dokokin Kano Ta Ce An Yi Rashin Adalci Wajen Ɗaukar Aikin Kwastam A Nijeriya

Majalisar Dokokin Kano Ta Ce An Yi Rashin Adalci Wajen Ɗaukar Aikin Kwastam A Nijeriya

October 30, 2025
SIN

Bai Kamata Gwamnati Ta Ke Ciyo Bashi Bayan Cire Tallafin Man Fetur Ba – Sanusi II

October 30, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.