Dan wasa Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa daga yanzu babu sauran adawa tsakaninsa da babban abokin hamayyarsa a fagen kwallon kafa, wato Lionel Messi, inda a cewarsa sun sauya tarihin kwallon kafar duniya. Ronaldo da Messi, ‘yan wasa biyu ne da ake yi wa lakabi da, ‘yan wasan da suka fi shahara a tarihi, wato ‘Gaot’ – sun sha fuskantar juna a lokacin da suke buga gasar La Liga a kungiyoyin Real Madrid da Barcelona.
Dan wasa Ronaldo ya ce dukkannin su ana girmama su a duniya, wannan shi ne babban abu mafi muhimmanci saboda haka lokaci ya yi da adawa a tsakanin su za ta zo karshe.
Ronaldo wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or har sau biyar – a bana baya cikin mutanen da ke takarar kyautar karon farko tun shekara ta 2003, yayin da Messi zai iya lashe kyautar karo takwas a tarihi.
“Ya kafa tarihi, ni ma na kafa nawa, ya yi abin da ya dace, daga abin da na gani,” in ji Ronaldo mai shekara 38 a duniya wanda a yanzu yake buga wasa a kungiyar Al-Nassr ta Saudiyya.
Dan kasar Portugal din ya ci gaba da cewa “bai kamata wadanda ke son Ronaldo, su ki Messi ba kuma a yanzu adawa ta kare, sun shafe shekara 15 suna jan zare a harkar kwallon kafa, don haka yanzu sun wuce abokai, sun zaman kwararrun abokan sana’a, kuma suna girmama junansu”.
‘Yan wasan sun cimma nasarori masu yawa a fagen wasan kwallon kafa, inda suka lashe kyaututtuka masu dimbin yawa a harkar kwallon kafa a matakin kungiyoyi da kasashe.
Ronaldo shi ne dan wasan da ya fi kowa zira kwallaye a Real Madrid inda ya ci 451 a wasa 438 da ya yi wa kungiyar, tare da cin kofuna 16 ciki har da Kofin Champions Leagues hudu da na La Liga biyu da na Copa del Rey biyu a tsowan shekara tara da ya yi a Real Madrid.
Shi kuwa Messi – wanda a yanzu ke wasa a kungiyar Inter Miami ta Amurka – ya kasance dan wasan da ya fi ci wa Barcelona kwallaye inda ya ci 674 a wasa 781 da ya buga wa kungiyar.
Messi – mai shekara 36 ya lashe kofuna 35 a Barcelona, ciki har da kofin La Liga 10 da kofin Champions League hudu da Copa del Rey bakwai a iya zaman da ya yi a kungiyar ta kasar Spaniya.
A matakin kasa kuwa Messi ya taimaka wa Argentina lashe Kofin Duniya da aka buga a Katar a 2022, sannan ya dauki kofin Copa America, yayin da shi kuma Ronaldo ya taimaka wa Portugal daukar kofin nahiyar Turai da kofin ‘Nations League’.
‘Yan wasan sun fuskanci juna a fili sau 36, haduwarsu ta karshe shi ne a watan Janairu a lokacin da kungiyar Messi ta PSG ta doke ta Al-Nassr da ci 5-4 a wasan sada zumunta.