Gwamnan Jihar Benuwe, Samuel Ortom, ya musanta labaran da ake yadawa cewar, kungiyar gwamnoni biyar, G-5 ta goyi bayan takarar Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa na PDP.
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan, Terver Akase ya fitar a ranar Talata.
- An Bai Wa Iyalan ‘Yansanda Da Suka Mutu A Bakin Aiki 43m A Anambra
- Aikin Hajjin 2023: Nijeriya Ta Kulla Yarjejeniyar Fahimtar Juna Da Gwamnatin Saudiyya
Sanarwar ta ce babu gaskiya a cikin labarin, kuma wani shiri ne a kokarin bata wa gwamnonin suna, inda ya bukaci jama’a da su yi watsayi da labarin.
Ortom a wata tattauna da ya yi da masu ruwa da tsakin jiharz ya jadadda cewar shugabancin jam’iyyar ya gaza yin adalci ga kowane tsagi bayan kammala zaben fidda gwanin da PDP ta gudanar.
G-5 dai sun shiga takun saka da Atiku wanda shi ne ya lashe zaben fidda gwanin da PDP ta gudanar a watan Mayun 2022, inda ya maka Wike da wasu a kasa.
Hakazalika, gwamnonin biyar sun bukaci a tsige shugaban jam’iyyar PDP, Iyorchia Ayu.
A baya Atiku ya yi kokarin yin sulhu da gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, lamarin da ya ci tura.