Sanata Oluremi Tinubu, matar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ta bayyana cewa mijinta ba shi da alhakin matsin tattalin arziƙin da Nijeriya ke fuskanta a halin yanzu.
Ta bayyana hakan ne yayin wata ziyarar da ta kai wajen Sarkin Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, ranar Alhamis, inda ta ƙaddamar da masauki ɗalibai da hanyar a Jami’ar Obafemi Awolowo.
- Shugaba Tinubu Ya Sake Aika Tallafin Buhun Shinkafa 18,500 Kebbi
- Yadda Muka Sanya Tinubu Ya Soke Kwangilar Aikin Hanyar Kankara Zuwa Katsina – Ibrahim Masari
Matsalolin tattalin arziƙi a Nijeriya sun ƙara ta’azzara tun bayan cire tallafin man fetur, wanda ya haifar da tashin farashin fetur daga N198 zuwa N1,030. Duk da haka, Uwargidan Tinubu ta kare gwamnatinsu, inda ta ce gwamnatin tana buƙatar lokacin domin watanni 18 kacal ta yi a ofis kuma tana aiki don gyara halin da ake ciki tare da tabbatar da makoma mai kyau ga ƴan Nijeriya.
Ta amince da cire tallafin amma ta nuna fata da cewa
“Cikin shekaru biyu masu zuwa, Nijeriya za ta fi yadda take yanzu.”
Uwargidan Tinubun ta kuma jaddada cewa mijinta ba mai son dukiya ba ne, sannan ta gode wa Allah saboda shugabancinsa. Ta bayyana cewa yana da wuya ga wanda yake da arziki ya zama shugaban ƙasa kuma ta yi alkawarin ba za su ba da kunya ba.
A lokacin ziyarar, ta ba da gudunmuwar Naira biliyan ɗaya ga makarantar da ta kammala karatunta, Jami’ar Obafemi Awolowo, don cigaban ta.
Sarkin Ife ya yaba wa Uwargidan Shugaban Ƙasar bisa kasancewarta abin koyi, musamman ga irin gudunmuwar da ta bayar lokacin da take Uwargidan Gwamnan Jihar Legas, inda ta kaddamar da tsare-tsaren da suka sa matasa sha’awar shiga sha’anin shugabanci.