Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sha alwashin cewa babu wani Kwamishina da za a nada ba tare da bayyana kadarorinsa ga hukumar da’ar ma’aikata ba.
Don haka gwamnan ya umarci dukkanin kwamishinonin da zai nada 19 da su bi ka’idojin da’a.
- Gwamnan Bauchi Ya Sake Nada Gidado A Matsayin Mashawarci Kan Yada Labarai
- Emefiele Ya Maka DSS A Kotu Kan Tsare Shi
Ana sa ran wadanda za a nada za su bayyana kadarorinsu akan lokaci kafin a tantance su da kuma tabbatar da majalisar dokokin jihar.
Gwamna Yusuf ya jaddada kudirinsa ga al’ummar jihar cewa gaskiya da rikon amana su ne ainihin ka’idojin gwamnatinsa, wadanda za a yi amfani da su wajen tsarin shugabanci na gari.
“Duk sauran masu rike da mukaman siyasa a karkashin wannan gwamnati su ma za su bi umarnin da aka ba su.
“Gwamna Yusuf na fatan kara jaddada aniyarsa ga mutanen jihar Kano cewa gaskiya da rikon amana ya kasance tushen tsarin gwamnatinsa wanda za a yi amfani da shi wajen tabbatar da kyakkyawan shugabanci kamar yadda ya yi alkawari a lokacin yakin neman zabe.” in ji Gwamnan.