Dan takarar majalisar dattawa na Yobe ta arewa karkashin jam’iyyar APC, Hon. Bashir Sheriff Machina ya bayyana cewa shi ne daliget suka zaba a matsayin dan takara a zaben fid da gwani na jam’iyyar APC a yankin arewacin Yobe, domin haka babu batun wani kuma ya zama dan takara.
Hon. Bashir Machina ya bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci dakin watsa shirye-shirye na Podcast na Kamfanin LEADERSHIP da ke Abuja.
Ya kara da cewa yana tabbatar wa jama’an da suka zabe shi a matsayin dan takarar da ma ‘yan Nijeriya cewa, zaben da aka gudanar yana nan daram kuma shi ne sahihin dan takara wanda jam’iyyar APC ta tsayar.
Ya dai musanta janye takararsa domin ya bai wa Sanata Ahmed Lawan, inda ya ce wannan labarin ba gaskiya ba ne. Ya ce babu wata magana irin wannan da ta taba faruwa tsakaninsa da Sanata Ahmed Lawan na ya janye masa takara.
Haka kuma ya bayyana cewa yana bukatar zama dan majalisar dattawa ne domin ya zamanantar da yanayin wakilci a matsayinsa na matashi duba da yadda Sanata Ahmed Lawan ya gudanar da tasa wakilcin na tsawon lokaci.
Sannan ya sha alwashin gudanar da wakilcin da ya dace da zai kawo sauki cikin karamin lokaci, domin ya tabbata yana da kwarewa da zai iya karawa daga inda Ahmed Lawan ya tsaya.
A cewarsa, shi dan siyasa ne mai biyayya ga uwar jam’iyya wanda ya kwashe tsawan shekaru 30 a cikinta, amma a cewarsa ita jam’iyya tana da ka’idoji da kuma dokoki wanda take tsayuwa a kansu, sannan da wannan dokokin ne ta bi wajen gudanar da zaben fid da gwani har ya samu nasara, saboda haka jam’iyya APC ba za ta taba cewa ya zo a yi wata magana da ta saba wa ko’idojinta ba.
Ya ce Ahmed Lawan ya bi ka’idoji ne har ya tsaya takarar shugaban kasa a karkashiun jam’iyyar APC, kuma shi ma wannan ka’idojin ne ya bi har aka zabe shi a matsayin dan takarar dan majalisan dattawa na yankin arewacin Yobe.
Hon. Bashir Machina ya ce jam’iyyar APC ta shaffida adalci wajen fitar da dan takarar shugaban kasa wanda har Bola Ahmed Tinubu ya samu nasara.
Ya ce idan ya samu damar zama dan majalisar dattawa na yankin arewacin Yobe zai yi kokarin hada kan jama’a wajen samar da tsaro a cikin jiharsa. Ya dai cewa matsalar tsaro ba za a iya magance shi ba har sai an hada hannu da karfe a tsakanin jami’an tsaro da kuma al’umma.
A cewarsa, yana da gwarin gwiwar lashe zabe a 2023, domin jama’a ne suka zabe shi a matsayin dan takarar sanata, sannan kuma jam’iyyarsa tana da gagarumin rinjaye a Jihar Yobe wanda zai iya samun nasara.
Ya ce a matsayinsa na dan siyasa zai dunga bin ra’ayin jama’a ne kan duk wani tsari da ya shafi wakilcinsa.
Har ila yau, Al’ummar Bade da Jakusko sun goyi bayan Hon. Machina.
A lokacin da takkadama ke ci gaba da zafafa tsakanin shugaban majalisan dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Ibrahim Lawan, da dan takarar Sanatan arewacin Yobe, Hon. Bashir Sharif Machina; biyo bayan kayen da Sanata Lawan ya sha a zaben fid da gwani na shugaban kasa da jam’iyyar APC ya gudanar a makon da ya gabata da kuma nasarar zaben fid da gwani da Machina ya samu a daya bangaren.
Wasu majiyoyi sun nuna cewa har yanzu Hon. Lawan yana hararar kujerar tare da bayyana bukatarsa ga Hon. Machina ya janye masa, bayan lashe zaben fid da gwani na takarar sanata na arewacin Yobe, al’amarin da ke ci gaba da daukar hankulan ‘yan Nijeriya.
A daidai wannan gabar, al’ummar kananan hukumomin Bade da Jakusko da ke Jihar Yobe sun fito kan tituna domin bayyana goyon bayansu ga takarar Hon. Machina, a tsakiyar wannan mako a garin Gashuwa, shalkwatar karamar hukumar Bade. Dubban jama’ar sun ziyarci fadar Sarkin Bade; Maimartaba Abubakar Umar Suleiman, domin mika gaisuwar girma tare da bayyana makasudin taron, wanda ya kunshi mata, matasa da masu ruwa da tsaki a siyasar yankin.
Da yake bayani ga manema labarai jim kadan da kammala taron, Barista Hamza Hashimu Karage, ya bayyana cewa, a matsayinsu na al’ummar masarautar Bade, sun yaba da hidimar da Sanata Ahmed Lawan ya yi wa kasa na kimanin shekaru 16 a zauren majalisar dattawan Nijeriya, inda har Allah ya kai shi zuwa shugaban majalisar, wanda hakan ba karamin abin alfahari bane ga al’ummar masarautar baki daya.
Bugu da kari kuma, ya ce “Muna alfahari da Sanata Ahmed Lawan bisa bajintar da yayi na takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar APC a zaben fid da gwani da ya gabata tare da bayyana bakin cikin rashin nasarar da ya yi a zaben.”
Ya ce, Hon. Bashir Machina gogaggen dan siyasa ne wanda ya samu nasarar zaben fid da gwani a kujerar Sanatan Zone C, wanda bisa hakan ne suke bayyana cikakken goyon bayansu gare shi domin samun nasara a babban zabe mai zuwa na 2023.
Ya ce, “Muna kira ga dukan ‘ya’yan jam’iyyar APC ciki har da na PDP da ke arewacin Yobe su goyi bayan Hon. Machina don samun gagarumar nasara a zabe mai zuwa. Kuma ina kara ba ku tabbacin cewa mu da matasa tare da dattawanmu a wannan yankin za mu hada hannu waje daya domin ganin Hon. Bashir Machina ya yi nasara.”
A nasa bangaren, tsohon shugaban karamar hukumar Jakusko, Hassan Kaku Lawan ya bayyana cewa, “Wannan taro ne na nuna goyon bayan al’ummar Bade da Jakusko ga dan takarar kujerar Sanatan Arewacin Yobe, Hon. Bashir Machina, wanda ya hada kowane bangaren jama’a, a matsayin yadda su ma al’ummar Machina da sauran kananan hukumomin wannan yankin suka mara wa namu Sanata a baya; Sanata Ahmed Lawan a shekarun da suka gabata.
“A hannu guda kuma, al’ummar wannan masarauta ta Bade suna bayyana cikakken goyon bayan su ga takarar Hon. Bashir Machina, bisa makamancin irin wannan goyon baya da suka samu daga masarautar Nguru da Machina a lokutan da Sanata Ahmed Lawan ya dauka yana rike da kujerar majalisar dattawan yankin, saboda haka muna goyon bayansa dari-bisa-dari.”
Shi kuwa tsohon mukaddashin sakataren tsohuwar jam’iyyar ANPP a Jihar Yobe, Mohammed D. Sa’idu (Gaskanta) ya tofa nasa albarkacin bakinsa da cewa, “Kamar yadda ka ce cin tuwon kishiya ramako, ko shakka babu haka zancen yake. Saboda kimanin shekaru 16 da suka gabata, ita ma masarautar Nguru ta rike kujerar Sanatan Arewacin Yobe, wanda an shirya wannan taron ne domin bayyana goyon bayan al’ummar Bade da Jakusko ga takarar Hon. Bashir Machina a matsayin rama hadin kai da goyon bayan da suka nuna mana a wadannan shekaru ga Sanata Ahmed Lawan.”
A nasa bayanin, shugaban taron kuma tsohon kwamishina a ma’aikatar wasanni da matasa ta Jihar Yobe, Mallam Saleh Kachalla ya bayyana makasudin taron da cewa, “A matsayinmu na al’ummar Bade da Jakusko; makasudin shirya wannan gangamin shi ne domin bayyana goyon bayanmu ga takarar kujerar Sanatan Arewacin Yobe wadda Hon. Bashir Sharif Machina zai yi, muna yi masa fatan alheri tare da samun goyon bayanmu a babban zabe mai zuwa a 2023.”
A hannu guda kuma, kwamitin yakin neman zaben Hon. Bashir Sharif Machina ya karyata bayanan da ke yawo a kafafen sada zumunta na zamani cewa Hon. Bashir Sharif Machina ya janye takararsa, wanda kwamitin ya bayyana wannan zance a matsayin maras tushe ballantana makama, tare da sake tabbatar wa jama’a cewa har yanzu dan takarar yana nan kan bakarsa na dan takarar Sanatan Arewacin Yobe a zaben 2023 mai zuwa.
A wata sanarwar manema labarai mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin, Alhaji Shehu Riga, ya bayyana cewa, “Babu wani lokaci a kowane yanayi da Hon. Machina ya taba sanya hannu ko bayani dangane da batun janyewa wani takarar da yake na kujerar Sanatan Arewacin Yobe. Saboda haka muna kira ga jama’a su yi watsi da wannan jita-jita marasa tushe ballantana makama.”