Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya kara tsawaita wa’adin amfani da tsofaffin takardun Naira har illa Masha Allah.
Babban bankin ya sauya takardun Naira N200, N500 da kuma N1,000 a watan Oktobar 2022 kuma an sanya wa’adin ranar 31 ga watan Disamba a matsayin ranar daina amfani da su.
Sai dai CBN ya za a ci gaba da amfani da kudin har abada, wanda ke nuni da cewa za a ci gaba da amfani da su.
“Babban bankin Nijeriya na son sanar da jama’a bukatarsa na tsawaita wa’adin dokar daina amfani da tsofaffin takardun N200, N500 da kuma N1,000.
“Don haka duk takardun kudin da babban bankin Nijeriya (CBN) ya fitar, bisa ga sashe na 20(5) na dokar CBN ta shekarar 2007, za su ci gaba da zama a dokance, har zuwa bayan wa’adin farko na ranar 31 ga Disamba, 2023. ,” a cewar daraktan sashen sadarwa na na CBN, Isa AbdulMumin.
AbdulMumin, ya ce babban bankin na hada kai da hukumomin da abin ya shafa don janye hukuncin kotun da ayyana wa’adin daina amfani da takardun kudin.
Ya ce duk rassan CBN da ke fadin kasar nan za su ci gaba da fitar da kuma karbar tsofaffin takardun Naira daga daidaikun mutane da kuma bankunan kasuwanci.
“An umarci jama’a da su ci gaba da karbar duk wasu tsofaffin takardun Naira don mu’amalar yau da kullum, “in ji shi.
Tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele ne ya sauya takardun Naira ana gab da shiga babban zaben 2023, lamarin da ya tada kura da cece-kuce a Nijeriya.