A lokacin da ya gana da jagororin muhimman kungiyoyin tattalin arzikin duniya a jiya da safe a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin ya bayyana ra’ayinsa game da tattalin arzikin duniya da na kasar Sin da ma batun kula da tattalin arzikin duniya da sauransu. Ban da haka, ya kuma bayyana matsayin da har kullum kasarsa ke dauka game da dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka, inda ya jaddada cewa, takaddamar haraji da cinikayya da fasaha ta saba wa tarihi da dokokin tattalin arziki, kuma babu wanda zai ci nasara daga gare ta.
A halin yanzu, duniyarmu ta shiga wani zamanin da ake fama da sauye-sauye, a yayin da kuma aka samu cikas a dunkulewar tattalin arzikin duniya. Kasashen yammacin duniya, musamman ma Amurka, sun fake da sunan “kare tsaronsu” suna ta rura wutar katse huldar tattalin arziki da wasu kasashe, a yunkurin kiyaye babakerensu a duniya, sai dai hakan ya lalata hadin gwiwar kasa da kasa ta fannin samar da kayayyaki da ma ingancin tattalin arzikin duniya, matakin da kuma ya saba wa burin sassan masana’antu da na kasuwa na fadin duniya.
Lallai rufe wa juna kofa ba zai amfanar da kowa ba, a maimakon haka, bude wa juna kofa shi zai samar da mafita. Nan da wata guda mai zuwa, za a samu sabuwar gwamnati a kasar Amurka. A gaban tarin kalubalolin da kasa da kasa ke fuskanta, daukacin duniya na fatan ganin huldar da ke tsakanin Sin da Amurka ta bunkasa yadda ya kamata, kuma su taka rawar da ta dace wajen kiyaye tsarin samar da kayayyaki a duniya. Kasancewar kasashen biyu wasu muhimman sassa biyu ne a tsarin samar da kayayyaki na duniya, dole ne su hada gwiwa da juna, ta hakan za su samar da alfanu ga duniya. (Lubabatu Lei)