Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya karyata cewar akwai baraka tsakaninsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Da yake jawabi a wajen gangamin yakin neman zaben shugaban kasa da aka gudanar a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara a ranar Asabar, Tinubu, ya yi alkawarin magance matsalolin tsaro da suka addabi jihar tare da kyautata tattalin arziki da bunkasa harkokin kasuwanci.
- ‘Yansanda Sun Kama Kasurguman ‘Yan Bindiga 2, Sun Ceto Mutane 7, Sun Kwato 2.1m Kudin Fansa
- Daga 2016 Zuwa 2020, An Kashe Dala Biliyan 6 Wajen Shigo Da Alkama -CBN
Ya gode wa al’ummar jih5ar Zamfara tare da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar bisa kyakkyawar tarba da suka yi masa.
“Na goyi bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari tun kafin shigarsa ofis. Zan ci gaba da kasancewa daga cikin magoya bayansa kuma abokai har zuwa ranar karshe da zai bar mulki.”
Ya yi jinjina da irin kokarin da shugaba Buhari ya yi wajen daidaita lamura a fadin kasar nan.
“Shugaban kasa ya yi nasa kokarin wajen kyautata Nijeriya. Tabbas ya taka rawar gani sosai.”
Tinubu, ya yi fatali da cewar akwai rashin fahimta a tsakaninsa da Buhari.
Ya tabbatar da cewa idan ya zama shugaban kasa zai yi hidima sosai wajen tabbatar da gyara kasar nan da ci gaba da tafiya da manufofi da tsare-tsare masu kyau da gwamnatin Buhari ta faro.
Ya yi wa al’ummar Jihar Zamfara alkawarin cewa matsalar tsaro za ta zama tarihi a karkashin mulkinsa.