Daya daga cikin dattawa mata a masana’antar Kannywood wadanda su ka dade ana damawa dasu kuma har yanzu suke haskakawa a masana’antar, a wata hira da aka yi da ita a dandalin Hadiza Gabon mai suna Gabon’s Room Talk Show ta bayyana cewar babu wata sana’a da ake samun daukaka da samun alheri kamar sana’ar fim.
Hajara Usman ko kuma Mama Hajo kamar yadda wasu ke kiranta ta tabbatar da cewar sana’ar fim ba sana’a ce karama ko kuma wadda ta kunshi nishadi kawai kamar yadda wasu ke kallo ba, sana’a ce babba da ya kamata duk wani wanda ya ke kika da niyyar shigowa cikinta ya tabbatar ya dauke ta da muhimmanci domin shima ya samu tarin alherin da yake a cikinta.
- Allah Ya Yi Wa Mawaƙin Kannywood, El-Mu’az Birniwa Rasuwa
- Tun Kafin A Samu Masana’antar Kannywood Nake Harkar Fim – Lilisco
Ina bayar da shawara ga yara da manya da ke da sha’awar shiga harkar fim da su tabbatar da cewar sun shigo da niyya daya, kuma su dauketa da muhimmanci sosai domin kuwa harka ce mai kyau ba yadda wasu ke daukatarta ba, wasu sun dauka cewar kawai ka fito a fim a kalleka idan ka tafi wajen taro yara su dinga ihu su na binka shi ne fim,wanda ko kusa wannan ba haka yake ba in ji Mama Hajara wadda ta shafe shekaru fiye da 20 ana damawa da ita a masana’antar.
Tunda farko dai ta bayyana cewar wannan masana’antar ta Kannywood ta yi mata komai a rayuwa domin kuwa duk wani abin alheri da sana’a za ta iya yi wa mutum to tabbas ta samu a wannan harka,saboda haka babu abinda za ta ce a kan wannan sai hamdala ga Allah madaukakin Sarki.
Dangane da yadda wasu manya a masana’antar ke dauka cewa ba su samun girmamawar da ta dace daga kananan jarumai a masana’antar, Hajara Usman ta ce a nata bangaren ba haka abin yake ba domin kuwa mata da maza a masana’antar Kannywood na matukar ganin girmanta kuma har gobe tana da kima a idonsu,don kuwa babu wani abu na raini da ya taba shiga tsakaninta da matasan jarumai.
A kan yadda wasu dattawa a masana’antar har wayau ke ganin basu samun daidaito wajen biyan kudin aiki duba da cewar sun tsufa ana ganin kamar matasa sun fi dacewa da a biya su kudade masu yawa,Mama Hajo ta ce duk wanda yake da irin wannan tunanin to ba a matsayin sana’a ya dauki harkar fim ba, don kuwa inda a matsayin sana’a ya dauki fim da ba zai yi wannan batun ba.
Ni a tunanina duk wanda ya dauki kudi ya baka a matsayin kudin sallama to ya na ganin su ne suka dace da kai, kuma ai sana’a ‘yar yau da gobe ce idan yau ka yi wa wannan aiki ya biyaka kadan gobe wancan zai biyaka da yawa idan ka yi mashi aiki, saboda haka ba na daukar wannan a matsayin wata matsala don kuwa kowane allazi da nashi amanu in ji ta.
Daga karshe ta yi karin haske dangane da yadda masana’antar Kannywood ta ke a lokacin baya da kuma yanzu inda ta ce a baya duk wanda ya yi fim zai dauka ya kai kasuwa ya siyar wa mutane, musamman wadanda suke zaune a karkara za su saye su kalla a gidajensu ko gidajen kallo da ake budewa a kauyuka, amma yanzu da ake dora fina finai a shafukan yanar gizo muddin ba babbar waya ka mallaka ba,ba lallai ne ka iya kallon sabon fim ba.
Saboda haka ta ce a nata tunanin da za a ci gaba da amfani da duka hanyoyin kallo ma’ana faifan cd da shafukan yanar gizo da abin zai fi,wanda zai iya kalla a faifan cd ya kalla haka zalika wanda zai tafi shafukan yanar gizo ya kalla shima sai ya kalla ba tareda wata matsala ba.