Gwamnatin Jihar Edo ta ce babu wata shaida da ke nuna akwai mayakan kungiyar ‘yan ta’adda ta ISWAP a kowane yanki na jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan sadarwa da wayar da kan jama’a na Edo, Chris Nehikhare ya fitar ranar Asabar, kuma ya mika wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a Abuja.
- An Nada Sanatan PDP Cikin Kwamitin Yakin Zaben Tinubu
- Tsananin Zafin Kaye A Zaɓen Fidda Gwani Yasa Wike Sambatu – Babba Mazoji
A cewar Nehikhare, harin da aka kai a mahadar titin Ibillo-Igarra, inda aka kona wata motar sintiri ta Wabaizigan ta ‘yansanda a ranar 22 ga watan Satumba, ‘yan bindiga ne suka kai harin, ba ‘yan kungiyar ISWAP ba.
“Bayan cikakken bincike da jami’an tsaro da suka hada da ‘yansanda, sojojin Nijeriya, kungiyar ‘yan banga ta Jihar Edo da kuma jami’an tsaron farin kaya na Nijeriya suka gudanar ya nuna babu wata shaida ta ISWAP ko mayakanta a jihar.
“Gwamnati ta ba da tabbacin cewa za ta ci gaba da bayar da tallafi ga jami’an tsaro a jihar domin magance miyagun laifuka.
“Sannan kuma za a inganta aikin sintiri a kan iyakokin jihar domin dakile ayyukan ‘yan bindiga.
“Gwamnatin Edo ta jaddada kudirinta na kare rayuka da dukiyoyi a jihar da kuma samar da yanayi mai aminci ga ‘yan kasa don gudanar da sana’o’insu,” in ji shi.