A ranar Litinin 13 ga Fabrairu, 2023 za a ci gaba da sauraron karar da aka shigar da dan dan uwan Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, Ali Bello da matarsa Rashida Bello kan badakalar karkatar da kudade a gaban Mai Shari’a Obiora Egwuatu na Babban Kotun Tarayya dake Abuja.
Ali Bello na daga cikin mutane hudu da aka kama a ranar 8 ga Fabrairu, 2023 kan tuhume-tuhume 18 da suka hada da almubazzaranci da kudade har naira Biliyan N3,081,804,654.00.
Sauran wadanda ake tuhumar su ne Abba Adauda, Yakubu Siyaka Adabenege da kuma Iyada Sadat.
Wadanda ake tuhumar dai, sun ki amsa laifin da ake tuhumarsu da su.
Dangane da kin amsa laifin da ake tuhumarsu da shi, lauya mai shigar da kara, Rotimi Oyedepo, ya bukaci kotun da ta kara musu wani lokaci domin gabatar da cikakkiyar hujja kan tuhume-tuhumen.