Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya amince da nadin wasu sarakunan gargajiya guda biyu a masarautar Yauri da ke a Jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata takardar manema labarai mai dauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu, Alhaji Muhammad Sani Umar, da aka rabawa manema labarai a Birnin Kebbi.
- Wasu Ma’aikata 3 Sun Lakada Wa Babban Alkalin Kotun Majistare Duka A Jihar Kebbi
- Kwastam Ta Kama Kayan Fasa Kwauri Da Kudinsu Ya Kai Miliyan 78.6 A Kebbi
A cewar sanarwar, sarakunan biyu da aka nada su ne, Muhammed Bello Na’Allah, a matsayin Uban kasar Makurdi a karamar hukumar Ngaski da Lawal Jibrin Yahaya a matsayin Uban kasar Kwanji a karamar hukumar Shanga ta jihar Kebbi.
Gwamnatin Jihar ta yi wa sabbin wadanda aka nada fatan Allah ya yi musu jagora da kariyarsa wajen gudanar da sabon aikin da aka dora musu.