Gwamnan Jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu, ya umarci sakataren gwamnatin jihar, Babale Umar Yauri, ya shiga tsakani kan rikicin da ya auku a makon da ya wuce tsakanin sojoji da ma’aikatan kamfanin samar wutar lantarki (KAEDCO) kan yanke wutar da ya shiga kwana uku a Birnin Kebbi.
Bagudu ya bayyana hakan ne a jiya Litinin a yayin da yake jawabi dakin taro da ke masaukin da ake sauke shugaban kasa da ke a Birnin Kebbi.
- Kwamandan Yaki Da ‘Yan Sara-Suka Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Zamfara
- Zazzabin Lassa Ya Yi Ajalin Mutum 154 A Nijeriya —NCDC
Ya ce, kamfanin ba zai iya gudanar da aikinsa idan masu amfani da wutar ba sa biyan kudin wutar da suka yi amfani da ita ba, inda ya kara da cewa, hakan zai zama abu mai wuya a samar da wutar mai dorewa a jihar.
Ya ce, “A baya muna samar da rangwame ga masu amfani da wutar, amma yanzu mun kai wani lokaci da ba za mu iya ci gaba da yin hakan domin muna samo kudaden ne daga cibiyoyi daban-daban.”
Tun a ranar Asabar din da ra gabata ne, kamfanin na KAEDCO ya yanke wutar da yake tura wa daukacin Birnin Kebbi saboda rikicin.
An ruwaito cewa, umarnin na gwamnan da ya bai wa sakataren gwamnatin jihar, ana sa ran zai tattauna a Barikin Dukku da mahukuntan kamfanin na KAEDCO da kuma mahukuntan sojin domin a lalubo mafita kan rikicin da ya janyo rashin samar da wutar a daukacin fadin babban birinin jihar.
Bugu da kari, wani babban jami’in soji da ke a Barikin Dukku a Birnin Kebbi wanda kuma ya nemi a sakaya sunansa ya ce, sojojin da suka je kamfanin na KAEDCO, ba su doki ma’aikaci ko daya ba.
A cewarsa, sojojin sun je kamfanin ne kawai domin su shigar da korafi da nuna bacin ransu kan rashin samar da wuta da kamfanin ke yi, inda hakan ya lalata kayan da matansu ke yin sana’a wanda sai da wutar ne za su iya gudanar sa sana’arsu.