Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dade yana kasuwanci, wanda kuma yake matukar son matsawa abokan takara lamba don tilasta musu mika wuya. A yanzu dai, yana fakewa da batun harajin kwastam don tilastawa kasashe shiga shawarwari, ta yadda zai ci moriyarsu.
Nuna fin karfi ne Amurka ke yi wajen kakaba harajin ramuwar gayya ga kasashen duniya, kuma bai dace ba a mika wuya gare ta ba. Asara kawai za a tafka muddin aka gudanar da ciniki a duniya bisa ka’idar nuna fin karfi. Dole ne kasashen duniya su nace ga tsarin gudanar da harkoki tsakanin mabambantan bangarori da hadin gwiwa da cin moriya tare, wadda ita ce hanya daya tilo da za a iya tinkarar ra’ayin kashin kai da manufar kariyar ciniki.
Game da yakin cinikin da Amurka ta kaddamar a duniya, tuni Sin ta bayyana matsayinta a fili, wato ba ta son ganin haka, amma kuma ba ta jin tsoro. In da gaske ne Amurka take son daidaita matsalar da ake fuskanta, dole ne ta daina yin barazana da zalunci, kuma ta koma yin shawarwari bisa tunanin adalci da daidaito da mutunta juna da kawo moriyar juna. (Mai zane da rubutu: MINA)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp