ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ta Yaya Za A Iya Tabbatar Da Tsaro A Yammacin Afirka?

by CGTN Hausa and Sulaiman
9 months ago
Tsaro

Shugaban majalisar kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afirka ta ECOWAS Omar Touray, ya bayyana a kwanan baya cewa, yanayin tsaro a yammacin Afirka na tabarbarewa cikin sauri, har ma ya riga ya kai wani matsayi na ta-baci.

A ganin ECOWAS din, wani babban dalilin da ya haddasa hakan shi ne rashin kwanciyar hankali a wasu kasashe. Misali, juyin mulki da bai samu nasara ba a kasar Benin, na ranar 7 ga watan da muke ciki, da juyin mulki da sojojin kasar Guinea-Bissau suka yi a karshen watan da ya gabata. Hakika bisa alkaluman da wasu kafofin watsa labarai suka gabatar, an ce cikin shekaru fiye da 10 da suka wuce, an samu aukuwar juyin mulki, ko kuma yunkurin kifar da gwamnati da bai yi nasara ba, a rabin kasashe mambobin kungiyar ECOWAS, ciki har da juyin mulki da aka yi a kasashen Mali, da Burkina Faso, da Nijar, tsakanin shekarar 2020 da 2023. Kana bayan da sojojin kasashen 3 sun kwace ragamar mulki, an fara samun tsamin dangantaka tsakanin wadannan kasashen da kungiyar ECOWAS, lamarin da ya sanya kasashen janye jiki daga ECOWAS a watan Janairun bana, tare da kafa kungiyar hadin gwiwar kasashen yankin Sahel ta AES.

Ban da haka, hare-haren ta’addanci su ma suna haifar da tashin hankali a yammacin Afirka. Bisa wani rahoto da cibiyar nazarin tattalin arziki da zaman lafiya ta kasar Australiya ta fitar, an ce cikin kasashe 10 da suka fi fama da hare-haren ta’addanci a bara, 5 suna yankin yammacin Afirka da na Sahel, inda adadin hare-haren ta’addanci da suka auku a yankin ya kai kaso 19% na adadin duniya, kana yawan mutanen da suka rasa rayuka a yankin sakamakon ta’addanci, ya kai kaso 51% cikin jimillar na duniya. Haka zalika, an ce a bana, a Najeriya kadai, kungiyoyin ’yan ta’adda irinsu ISWAP, da Boko Haram, sun kaddamar da hare-hare fiye da 300. Inda ayyukan ta’addanci suka haifar da bazuwar makamai, da rashin tsari da oda, a kauyuka da kananan hukumomi, lamarin da ya ba ’yan fashin daji karin damammakin tayar da zaune-tsaye.

ADVERTISEMENT

Yanzu haka a jihar Zamfara ta Najeriya, hare-haren ’yan fashin daji sun lalata yanayin rayuwar dimbin mutane mazauna kauyuka, da tilastawa dubun-dubatar mutane kama hanyar gudun hijira, yayin da tashin hankali ke ci gaba da bazuwa zuwa jihohin makwabta irinsu Sokoto, da Kebbi, da Kaduna, da dai sauransu.

To, ko ta yaya kasashen yammacin Afirka za su iya tinkarar matsalar tsaro? Dangane da wannan tambaya, shahararren masanin ilimin siyasa na kasar Ghana Paul Frimpong, ya bayar da shawarar a nemi amsa daga shawarar tabbatar da tsaron duniya ta (GSI) wadda kasar Sin ta gabatar.

LABARAI MASU NASABA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

Wannan shawara ta Sin ta jaddada muhimmancin tabbatar da tsaro na bai daya mai dorewa, bisa hadin gwiwar bangarori daban daban, da mayar da hankali kan damuwar duk wata kasa, da girmama mulkin kai, da neman daidaita rikici da ayyukan ta’addanci ta hanyar tattaunawa da hadin gwiwa. A ganin Mista Frimpong, shawarar GSI da kasar Sin ta gabatar tana iya ba da taimako wajen kawar da sabanin ra’ayin da ake samu tsakanin kungiyoyin ECOWAS da AES, da kulla alaka mai karfi ta hadin kai a tsakanin kasashen yammacin Afirka, ta fuskar dakile ta’addanci da tabbatar da kwanciyar hankali.

Hakika matukar an yi hadin kai, to, tabbas hakan zai haifar da sakamako. Misali, daga watan Maris na shekarar 2024 zuwa watan Yuli na shekarar 2025, kasashen Najeriya, da Nijar da Chadi, sun dauki matakin soja na hadin gwiwa, mai taken “Garkuwar Sahel”, don yaki da kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi, inda aka kashe ’yan ta’adda fiye da 1200, ciki har da madugansu fiye da 80, da rushe maboyar ’yan ta’adda 37, tare da rage yawan laifukan sace mutane dake aukuwa a kan iyakar kasashen 3 da kaso 40%. Ban da haka, a yayin da ake tinkarar yunkurin juyin mulki a kasar Benin a kwanakin nan, tallafin soja da Najeriya da sauran mambobin kungiyar ECOWAS suka bayar, shi ma ya taka muhimmiyar rawa wajen maido da kwanciyar hankali a kasar Benin.

Sa’an nan kasashen yammacin Afirka, su ma za su iya hadin gwiwa da kasashen dake wajen nahiyar, misali kasar Sin. A wajen wani taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, kan batun yaki da ta’addanci a yammacin Afirka da yankin Sahel, wanda ya gudana a watan da ya gabata, wakilin kasar Sin ya yi alkawarin cewa, Sin tana tsayawa tsayin daka wajen nuna cikakken goyon baya ga kasashen Afirka, a fannin wanzar da zaman lafiya da tsaro, kuma za ta karfafa hadin gwiwarta da yammacin Afirka, da yankin Sahel ta fuskar dakile ta’addanci, don samar da karin gudunmowar kare zaman lafiya da tsaro a yankunan, gami da a duk nahiyar Afirka gaba daya.

Hausawa su kan ce, tsintsiya daya ba ta shara. Tabbas, shawarar GSI da kasar Sin ta gabatar, ita ma ta nuna irin wannan ra’ayi. Muna fatan ganin kasashen yammacin Afirka sun karfafa hadin kansu, da kokarin hadin gwiwa da abokan hulda na sauran sassan duniya, ta yadda za su iya cimma burinsu na tabbatar da tsaro, da kwanciyar hankali a yankin da suke ciki. (Bello Wang)

Tsaro
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa
Tsaro
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa
Ra'ayi Riga

Samun Rarar Kudin Ciniki Ba “Laifi” Ba Ne, Hadin Gwiwa Da Cin Moriya Tare Ita Ce Mafita Ga Kowa

September 2, 2026
Next Post
Bunkasar Masana’antun Kasar Sin Ya Kai Kaso 6.0% a Watanni 11 Na Farkon Shekarar Bana

Bunkasar Masana'antun Kasar Sin Ya Kai Kaso 6.0% a Watanni 11 Na Farkon Shekarar Bana

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.