Sanin kowa ne cewa kafin a fara aiwatar da duk wani irin aiki, dole ne a tantance ko ya dace ko bai dace ba, musamman ma game da muhimman ayyukan da ke shafar rayuka da lafiyar al’umma irinsu zubar da ruwan dagwalon tashar nukiliya ta Fukushima a cikin teku.
Duk da haka, daga cikin dukkanin shirye-shirye da take iya zaba na sarrafa ruwan dagwalon, gwamnatin Japan ta zabi shirin zubar da ruwan cikin teku, saboda tsimin kudi da kuma rashin haifar da barazanar gurbacewar muhalli ga ita kanta, duk da hasarar da hakan ya haifarwa sauran kasashen duniya.
Idan ba a manta ba, a ranar 11 ga watan Maris na shekarar 2011, an yi girgizar kasa mai karfin maki 9 a tekun da ke arewa maso gabashin kasar ta Japan, girgizar da ta lalata tashar nukiliya ta Fukushima, har ma ta haddasa yoyon dimbin sinadaran nukiliya daga tashar. Ya zuwa shekarar 2021 kuma, gwamnatin Japan ta sanar da shirinta na zubar da ruwan dagwalon tashar nukiliya ta Fukushima a cikin teku bisa dalilinta na yadda ruwan ya kai iyakar da take iya adanawa, matakin da nan da nan ya jawo suka daga gamayyar kasa da kasa.
Me ya sa kasa da kasa suka soki shirin na Japan? Sabo da ruwan dagwalon tashar Fukushima na kunshe da sinadaran nukiliya masu guba sama da 60. Ga shi kuma igiyar ruwa da ake samu a mashigar tekun Fukushima na da matukar karfi.
An ce da zaran an zubar da ruwan, zai iya bazuwa zuwa sama da rabin tekun Pasifik cikin kwanaki 57, da ma tekunan duniya baki daya cikin shekaru 10. Don haka, bai kamata a kawar da kai daga mummunan tasirin da zai iya haifarwa ga yanayin teku da ma tsaron abinci da kuma lafiyar bil Adama ba.
Duk da haka, Japan ta yi ta kare aniyarta na aiwatar da shirin, tare da neman wanke kanta ta kowa ce hanya. Sai dai in da gaske ne ruwan dagwalon da take son zubarwa a cikin teku ba shi da illa, me ya hana kasar barin ruwa don yin amfani da shi wajen noma da sauran harkoki, ko kuma ta zuba su cikin tabkunanta?
Hakika, zubar da ruwan dagwalon ba batu ne da ya shafi kasar Japan ita kadai ba, batu ne da ya shafi duniya baki daya. Son kai na Japan ya iya haddasa hadari da ma illoli ga sauran kasashen duniya.
Yanzu haka, wata tawagar masana ta hukumar makamashin nukiliya ta duniya(IAEA) na yin ziyarar aiki ta kwanaki 5 a kasar ta Japan, muna fatan masanan na IAEA za su yi bincike kan wannan shiri na Japan bisa sanin ya kamata, da adalci, a kokarin kiyaye tsaron kasa da kasa.
Duniya na kalubalantar Japan da ta sauke nauyin da ke bisa wuyanta, ta yi cikakken shawarwari tare da masu ruwa da tsaki, don daidaita batun cikin tsaro kuma yadda ya kamata. (Lubabatu Lei)