Biyo bayan bullar annobar zazzabin Lassa a Adamawa, kwamishinan ma’aikatar lafiya ta jihar, Felix Tangwami, ya shawarci Jama’a da cewa bai kamata su tsorata ba, a cewarsa gwamnati ta dauki matakan da suka dace.
Kwamishinan wanda ya bayyana haka a taron manema labarai a Yola ranar Litinin, ya ce ma’aikatar ta sanar da barkewar cutar biyo bayan wani tabbataccen binciken wani samfurin kwayar cutar da cibiyar bincike ta kasa (NRL), ta gudanar kan wani matashi dan bautar kasa (NYSC) a jihar.
“Duk da cutar zazzabin Lassa cuta ce mai saurin yaduwa tsakanin jama’a, ana kamuwa da kwayar cutar ta hanyar taba abinci ko kayan gida da su ka gurbata da najasar berayen da su ka kamu da cutar.
“Zazzabin na haifar da raunin gabobi bakidaya da rashin lafiya, ciwon kai, ciwon makogwaro, ciwon tsoka jiki, tashin zuciya, amai, gudawa, tari da sauran matsaloli” in ji Tangwami.
Felix Tangwami ya ce ma’aikatar lafiyar jihar ta bukaci babban daraktan cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta kasa (NCDC), da ya ba su damar kai samfurin cutar zuwa dakin gwaje-gwajen kwayoyin halittar cututtuka da ke Bauchi.
Ya kuma kara da cewa ma’aikatar ta nada kwamitin lafiya wanda a shirye yake don shawo kan duk wani irin kalubalen kiwon lafiya a jihar.
Da yake magana kan barazanar cutar sankarau har ila yau, kwamishinan ya bukaci jama’a da su nisanta kansu daga wuraren da ake fama da cunkoso a wannan lokacin zafi, kuma a koda wani lokaci su rika zama wurin da ya kamata domin samun cikakkiyar iskar shaka.