Ministan kula da cinikayya da kasashen waje na Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, DRC Jean-Lucien Bussa Tongba, ya ce baje kolin harkokin tattalin arziki da cinikayya na Sin da Afrika karo na 3, ya gabatar da dimbin damarmaki ga kasarsa, wadda take daukar Sin a mastayin muhimmiyar abokiyar hulda.
Yayin wata tattaunawa da Xinhua gabanin tasowarsa zuwa kasar Sin, Bussa Tongba ya ce kasarsa na daukar taron baje kolin da muhimmanci. Baje kolin zai gudana ne daga 29 ga wata zuwa 2 ga watan Yuli a Changsha, babban birnin lardin Hunan na kasar Sin.
Kasar Sin ta kasance babbar abokiyar cinikayya ga Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, haka kuma mai zuba jari a kasar na lokaci mai tsawo.
A shekarar 2022, darajar cinikayya tsakanin kasashen biyu ta kai dalar Amurka biliyan 21.898, wanda ya karu da kaso 51.7 a kan shekara ta 2021. Haka kuma kasar Sin ta dauke haraji kan kaso 97 na kayayyakin Jamhuriyar Congo dake shigowa kasar, bisa wata manufar cinikayya mai bayar da fifiko. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp