Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr, Cristiano Ronaldo, ya caccaki kyautar Ballon d’Or ta UEFA da kuma kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya da hukumar FIFA ke bayarwa.
Inda ya bayyana cewa kyautar gwarzon dan kwallon kafa da ake bayarwa a yanzu ta rasa kimarta.
Tsohon fitaccen dan wasan Manchester United da Real Madrid ya soki lamirin yadda Lionel Messi ya lashe duka kyautukan biyu, yana mai nuni da cewa, ya kamata a bashi daya daga cikinsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp