A ƙalla mutane huɗu sun mutu yayin da wasu 21 suka jikkata sakamakon fashewar bama-bamai biyu da ‘yan ta’addar ISWAP suka dasa a ƙaramar hukumar Gujba ta jihar Yobe.
Fashewar ta farko ta faru ne da safiyar ranar Juma’a a hanyar Goniri-Buni Yadi, inda wata motar kasuwanci da ke ɗaukar ƴan kasuwa zuwa kasuwar Buni Yadi ta taka wani bam da aka dasa kusa da ƙauyen Bultaram.
- Sojoji Sun Kashe Babban Kwamandan Boko Haram A Jihar Yobe
- Hisbah Ta Rufe Otal, Ta Kwato Ƙwalaben Giya 209 A Yobe
Mutane uku sun mutu a asibitin kwararru na jihar Yobe da ke Damaturu, yayin da wasu 21 ke ci gaba da jinya.
Ƴan sa’o’i bayan haka, wani ɗan keke da ba a san ko wanene ba ya taka wani bam a yankin, inda ya mutu a asibitin Buni Yadi.
Jami’an tsaro da na agajin gaggawa sun yi aikin share hanya don hana ƙarin ɓarna, yayin da aka ci gaba da binciken yankin.