• English
  • Business News
Sunday, June 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bambancin Bukukuwan Sallar Bara Da Ta Bana

by Sulaiman
5 hours ago
in Al'adu
0
Bambancin Bukukuwan Sallar Bara Da Ta Bana
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shafin TASKIRA na yi wa daukacin al’ummar musulmi barka da sallah, da fatan kowa zai kammala bikin sallah lafiya.

Kamar kowane mako wannan shafi ya kan zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, shafin mu na yau zai yi duba ne game da; Bambancin sallah ta Bara da kuma sallah ta Bana, inda shafin ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu; “Ya bambancin Sallar Bara da ta Bana take a wurarenku?, a wasu wuraren wasu mutanen na yin layya ba tare da sun bawa kowa ba, yayin da wasu ke ganin yin hakan babban kuskure ne yin layya ba tare da an sadakar ko da kuwa kowa yana da shi ba, me za a ce a kan hakan?, Ta wacce hanya iyaye mata za su kula da naman sallah domin gudun kar ya lalace da wuri?, Fadi hanyoyin sarrafa naman sallah wanda aka sani. Wacce shawara za a bawa wadanda ba su samu damar yin layya ba?”.

Ga dai bayanan nasu kamar haka;

Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor), Jihar Kano:

Gaskiya sallar bana ai sai godiya komai ya tsefe kai duk da tsadar sai mu ce Alhmadulillah. Hmmm to ita layya dama ai sadaka ce amma za ki ga wasu basu bayar wa sai a soye naman ko a boye a ‘frigde’ abin da ka bayar dai shi ne rabonka. A soye shi ya soyu sannan in ya huce abi shi da kakile a zuba a adana, kamar a soya ayi dambu, kilishi, gashi da kuma tsire. To abin da Allah ya sa suka samu na sadaka sai a soyawa yara in kuma ba a samu ba ayi hakuri.

Labarai Masu Nasaba

GORON JUMA’A 30-03-2025

GORON JUMA’A 16/05/2025

 

Sunana Abba Abubakar Yakubu, daga Jos ta Jihar Filato:

Akwai bukatar a tausayawa mabukata a lokacin layya.

Ita layya, wani yanki ne na ibada, wanda Allah Ta’ala ya dora akan bayinsa masu hali. Malamai sun koyar da mu rabe-raben irin dabbobin da ake so a yi layya da su, da kuma yadda ya kamata a yi yankan har da rabon naman. Sai dai ba kowa ne ke samun zarafin yin layyar ba, saboda halin rayuwa. Don haka ne ma addinin Musulunci ya koyar da muhimmancin rabon naman don sadaka da wani sashi ga wadanda ba su samu damar yin layya ba, da kuma wanda iyali ko iyaye za su yi amfani da shi. Kuskure ne mu rika zaton kowa ya samu damar yin layya, ko kuma ai makwafcina wane ya yi layya, saboda ina masa zaton yana da rufin asiri, ko kuma a baya ya saba yi duk shekara. A gaskiya yadda al’amura suka sauya yanzu, mutane suna cikin wani hali. Abin da ka fi karfi a baya, a yanzu ya fi karfin ka. Da dama daga cikin mutane an koma neman abin da za a ciyar da iyali kawai. Kuma ba kowa ne yake iya zuwa ya bude cikinsa don a taimaka masa ba. Don haka kirana ga masu hali da wadanda Allah ya hore wa ikon yanka abin layya, don Allah a tuna da makwafta da mabukata, da ‘yan’uwa na nesa da na kusa. Wadanda ke da halin yanka saniya ko raguna biyu ko uku, a wadata iyali da nasu, kuma a basu wanda za su bai wa nasu ‘yan’uwan, kai ma maigida ka raba wa naka, har da abokai da basu da karfi ko wadanda aka tashi tare. Ga wadanda suka samu damar yin layya ko suka samu wadatar naman sadaka, a soya na soyawa a ajiye a cikin kakile, ko a tafasa, ko a shanya, don kada ya yi saurin lalacewa. Sannan za a iya gasawa don kyafe ruwan jiki, saboda ya kwana biyu ana amfani da shi. Na gode

 

Sunana Ladifa Yusuf Bauchi A Nijeriya:

A gaskia akwai bambanci musamman yadda rayuwarnan ta kara tsada fiye da bara, hakan ya taba siyan abun layya, dan a wadansu wuraren ma za ki ga ragon sallah ya kai kimanin Naira dubu dari bakwai da hamsin. A addinin musulunci bai taba kaoyar da rowa ba sai dai ma ya koyar da yadda za ka bawa wanda bai samu ba shi ma ya samu, dan haka ya ce a raba nama zuwa ga mabukata, ‘yan’uwa, makofta, da abokan arziki, fan hakan na kara abubuwa da yawa. Kuma su sani yau idan suna da shi ba lallai ne gobe suna da shi ba, wataran ma gurinsu za su je nema. Hanyar da iyaye mata za su bi ita ce; Su tabbatar da cewar sun sulala naman a kalla 165°F (74°C) dan kashe kwayoyin cututtuka, Idan Allah ya wadata ki da ‘fridge’ to ki samu ki dibi wadansu daga cikin danyen naman ki kankare shi dan amfanin gaba. Ana iya sarrafa nama musamman naman sallah mai yawa ta hanyoyi dama kamar su; Kilishi, suya, farfesun naman kai, gasasshen nama da dai sauransu. Su tuna da cewar da sun niyya a zuciyarsu, dan Allah da zuciya yake amfani ba da jikkuna ba. Kuma mutum yanayin abun da Allah ya hore masa.

 

Sunana Aminu Adamu Malam Maduri A Jihar Jigawa:

To magana ta gaskiya shirin sallah ta bana sai muce Alhamdullilah domin raguna sun yi tsada sosai, ba kamar bara ba don haka ne ya sa al’umma da dama suka hakura. Eh tabbas wasu mutane suna yin haka, kuma tabbas kuskure ne domin ita layya sadaka ce don haka mutane ba a so su ci su kadai. To iyaye mata suke kula da wannan bangare, to amma kamata yayi su soya shi ya soyu sosai, kuma a zuba masa kakilai hakan zai taimaka wajen magance matsalar lalacewa. To na farko dai akwai soyawa, jargi, dambun nama, gashi dafawa duk ana yi wa naman sallah. To kamata ya samu ko dan kafizuru ne domin ya yankawa iyalan sa suma su dan samu su taba.

 

Sunana Hafsat Sa’eed daga Naija:

Bambancin sallar bara da ta bana akwai bambanci sosai ba kadan ba, duba da halin da ake ciki na matsin rayuwa, dan mafi akasari da dama wasu ma ba su yi layyar ba, wasu kuma abin da ya sa ba sa raba nama shi ne; idan iyalan da yawa a tawa fahimtar kenan, ina ga ko iya gidanka ka dan fitar ka bayar kamar ka ba da sadaka ne. Yadda ake yi dafa nama dan kar ya lalace shi ne, idan ka dafa naman sai a saka shi a cikin wani kitse da ake kira kakile, to ko da shekara nawa za a yi ba abin da zai yi.

 

Sunana Comr, Nr. Ibrahim Lawan Stk, Sule Tankarkar, Jihar Jigawa:

Wannan Sallah ta bana ta zo da kalubale da haka nake mata take da AWO YA KORI SIYAN NAMA, kalubalen wadanda suka hada da; rashin samun damar siyan abin layya akan sallah bara duba da yanayin farashin abin yanka a inda duk mafi akasarin mutane babu kudi a hunnunsu wanda a yanzu haka a halin da ake ciki mutane da dama na fama da neman hanyar samun abin da za su ci, ba ma ta nama ake ba hakan ya sa mo asali ta tsefewar farashin dabbobi tun kafin zuwan wannan lokaci na sallah wani abu ma da zai ba wa mutane mamaki shi ne dabbobi na tashin doron zabuwa tun lokacin da aka cire tallafin man fetir wanda hakan kan shafar farashin izuwa matakin kudi da yawa na tsada duk lokacin bukukuwan Sallah layya da kuma sallar kiristoci wadda akafi sani da kirsimati, wani abun mamakin ma shi ne ba ma ga sallah ba an haifi yara da yawa wanda har izuwa yanzu basu samu abin yankan suna ba saboda tsadar dabbobi, a shekarar bara da ta gabata mafi akasari mutane sun yi yankan sallah layya amma a yanzu ba ma tunanin yi saboda bambancin farashi abin yanka wanda a yanzu sun yi tsada ba kamar shekarar da ta gabata ba. Kamar yadda yakasance a al’adance haka kuma a addinance sadakar naman sallah layya abu ne mai kyau amma a halin da ake ciki yanzu ba kowa bane zai iya aiwatar da hakan duba da yawan mutane a cikin iyali da kuma irin dabbobi da ake yankawa a baya mutane da yawa na yanka babbar dabba kamar saniya amma a yanzu yanayi ya sa sai dai karmar dabba hakan zai sa mutane da yawa rashin aiyawatar da sadakar nama.

 

Sunana Princess Fatima Mazadu Gomben Najeriya:

To gaskiya sai godiya, amma na bana kam ya zo ba kudi ga yanayin rayuwa da kowa ke fama da ita, wanda da yawa dai akwai niyyar sauka layyar bana, saboda rashin wadaceccen abinci da masarufi wasu kuma tsadar dabbobin ne. Gaskiya kowa da irin al’adarsa, wasu suna ci ne dan suna samun yawan nama daga bana sai badi, wasu kuma suna kin kyautarwa ne dan rowa, wasu kuma saboda yaransu su ci ya gamshesu, sadaka ita ce daidai kamar yadda manzon Allah (SAW) ya ce; duk abun da ka sadakar shi ne guzurinka na kiyama, da yawa kam suna sadakarsa kuma suna kyautar wa makusantansu.

 

Sunana Muktari Sabo Jahun A Jihar Jigawa:

Tabbas sallar bana tasha bamban da ta bara ta bangaren sayen abin layya domin a bana layya ba duk kai bace domin ba kowane zai iya sayan abin layya ba. Eh ana samun masu yin layya don kansu yin hakan layya tayi amma ba haka aka so ba yadda ake so shi ne; idan kayi layya ka ci daga naman kayi kyauta ga makusantanka kuma kayi sadaka kena za ka yi abu uku ci, kyauta, sadaka. Za a kula da naman layya ne ta hanyar yi masa gyara mai kyau Idan an yi haka ba zai lalace da wuri ba. Wadanda basu sami damar yin layya ba su kwantar da hankalinsu domin Annabi (S A W) yayi magana su yi amfani da abin da aka samu na sadaka ko kyauta.

 

Sunana Muhammad Isah Zareku Miga Jihar Jigawa:

Bambanci tsakanin sallar bara da ta bana shi ne; Sallar bana ta zo da rashin kudi sai dai akwai saukin tsadar raguna saboda babu kudin za ka ga an tara raguna babu masaya sabanin ta bara akwai kudin amma akwai tsadar raguna. Eh wasu gureren sukan yi layya bata re da sun bawa kowa ba amma ni a gari na ba haka bane kusan duk naman layya sadakar da shi ga ke a masu karamin karfi wato wanda basu da halin yin layya. Hanyoyin kula da Naman layya don kar ya lalace ana yin danbum nama da kuma soyawa, ko kuma ayi jarginsa.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Amfanin Ganyen Mangwaro Ga Masu Ciki

Next Post

Rashin Abinci Na A Waka Ya Sa Na Daina Yi -T Y Shaba

Related

GORON JUMA’A 09/05/2025
Goron Juma'a

GORON JUMA’A 30-03-2025

1 week ago
GORON JUMA’A 16/05/2025
Goron Juma'a

GORON JUMA’A 16/05/2025

3 weeks ago
GORON JUMA’A
Goron Juma'a

GORON JUMA’A 28-03-2025

2 months ago
GORON JUMA’A
Goron Juma'a

GORON JUMA’A 14-02-2025

4 months ago
GORON JUMA’A 12-12-2024
Goron Juma'a

GORON JUMA’A 9-01-2025

5 months ago
GORON JUMA’A 12-12-2024
Goron Juma'a

GORON JUMA’A 3-01-2025

5 months ago
Next Post
Rashin Abinci Na A Waka Ya Sa Na Daina Yi -T Y Shaba

Rashin Abinci Na A Waka Ya Sa Na Daina Yi -T Y Shaba

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Alhamis, 12 Ga Yuni A Matsayin Ranar Hutu

Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Alhamis, 12 Ga Yuni A Matsayin Ranar Hutu

June 8, 2025
Wakilin Sin Ya Bayyana Rashin Gamsuwa Da Yadda Amurka Ta Gabatar Da Daftarin Kudurin Kwamitin Sulhu Kan Sudan Ta Kudu

Bangarorin Sudan Da Ke Dauki Ba Dadi Sun Zargi Juna Da Kai Hari Kan Jerin Gwanon Motocin MDD

June 8, 2025
Rashin Abinci Na A Waka Ya Sa Na Daina Yi -T Y Shaba

Rashin Abinci Na A Waka Ya Sa Na Daina Yi -T Y Shaba

June 8, 2025
Bambancin Bukukuwan Sallar Bara Da Ta Bana

Bambancin Bukukuwan Sallar Bara Da Ta Bana

June 8, 2025
Amfanin Ganyen Mangwaro Ga Masu Ciki

Amfanin Ganyen Mangwaro Ga Masu Ciki

June 8, 2025
Yadda Man Bilicin Ke Yi Wa Fatar Mutum Illa

Yadda Man Bilicin Ke Yi Wa Fatar Mutum Illa

June 8, 2025
An Daure ‘Yan Nijeriya Uku Shekaru 15 A Bisa Laifin Zamba A Indiya

An Daure ‘Yan Nijeriya Uku Shekaru 15 A Bisa Laifin Zamba A Indiya

June 8, 2025
Tattaunawar Da Shugabannin Sin Da Amurka Suka Yi Ta Wayar Tarho Ta Ba Da Jagoranci Ga Dangantakar Dake Tsakanin Kasashen Biyu

Tattaunawar Da Shugabannin Sin Da Amurka Suka Yi Ta Wayar Tarho Ta Ba Da Jagoranci Ga Dangantakar Dake Tsakanin Kasashen Biyu

June 7, 2025
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

An Kama Magidanci A Bauchi Bisa Zargin Lalata Da Agolarsa

June 7, 2025
Dabarar Yaudara Ta Kasar Philippines Kan Batun Tekun Kudancin Sin Ta Fito Fili

Dabarar Yaudara Ta Kasar Philippines Kan Batun Tekun Kudancin Sin Ta Fito Fili

June 7, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.