Napoli ta mayar da martani ga wani faifan bidiyo na TikTok mai cike da cece-kuce akan dan wasanta kuma dan Najeriya, Victor Osimhen.
A wannan makon, an ba da rahoton cewa Osimhen na iya daukar matakin shari’a a kan Napoli saboda wani faifan bidiyo na TikTok wanda yake shagube akan Osimhen saboda ya barar da bugun fanareti yayin karawa da Bologna a wasan Seria A.
- Osimhen Na Shirin Karar Napoli Kan Wani Bidiyonsa Da Suka Dora Akan TikTok
- An Nada Christopher Sabon Kocin Tawagar Kwallon Mata ‘Yan Kasa Da Shekaru 20 Ta Nijeriya
Amma, kungiyar ta Serie A a cikin wata sanarwa ta ce ba za ta iya yi wa Osimhen shagube ba, wanda ta ke daraja shi a matsayin dan wasa.
Idan Victor na ganin wannan shagubene akansa to wannan ba shine abin da kulob din ya nufa ba.
Idan zaku tuna Leadership Hausa ta bayyana cewar a ranar Talata da yamma, wakilin Osimhen Calendar ya bayyana cewar zasu dauki matakin shari’a akan kungiyar.