Maimuna Tijjani Iyam na daya daga cikin marubutan littattafan Hausa a yanar gizo masu tasowa. A ttaunawarta da Wakiliyarmu Princess Fatima Zarah Mazadu ta bayyanawa masu karatu dalilin da ya sa ta fara rubutu har ma da bangaren da ta fi karkata wajen yin rubutun, har ma da wasu batutuwan masu yawa. Ga dai Yadda tattaunawar ta kasance:
Masu karatu za su so su ji cikakken sunanki?
Sunana Maimuna Tijjani Iyam
Ko za ki fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?
Da farko kamar yadda na fada sunana Maimuna Tijjani Iyam haifaffiyar jihar Yobe cikin karamar hukumar Potiskum, a nan nayi makaranta tun daga kan ‘Nursery School’ har yanzu da nake matakin kama da ‘Secondary’ ina karatu a ‘Federal College Of Education Potiskum’ ina karantar ‘Computer/Biology’.
Me ya ja hankalinki har ki ka fara rubutu?
Gaskiya tun ina karama na tashi da sha’awar rubutu da kuma karance-karance, tun ba iya rubutun hausa ba nake kwatanta rubuta labari ta hanyar zanen hoto har na iya, a takaice dai sha’awa da son ba wa al’ummata gudumawa shi ya ja hankali na tsunguma harkar rubutu.
Za ki shekara nawa da fara rubutu?
Na fara rubutu tun ina aji uku a ‘Primary’ tun lokacin hausar bata gama zauna mini dai-dai ba wajen rubutata a rubuce.
Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?
An sha gwagwarmaya amma yanzu Alhamdulillah, matsalar farko da na fara cin karo da ita shi ne kafin a amince mini a gida na fara rubutun kasancewar karancin shekaruna a lokacin.
Kina so ki ce iyayenki ba su amince da fara rubutunki ba?
Gaskiya an nuna rashin amincewa don cikin wasa na fara sanar da mahaifiyata amma sai ta nuna mini bata so, duk da ita ma ma’abociyar karance-karance sosai, sai daga baya kuma na samu amincewar su wanda yanzu Alhamdulillahi.
Kamar wanne bangare ki ka fi maida hankali akai wajen yin rubutu?
Na fi mai da hankali game da abubuwan da suke faruwa a rayuwar mu ta yau da kullum, kuma duk wanda ya karanta littafina ya san hakan, gaskiya ban fiye gina jigon labari cakocam akan soyayya ba.
Kin rubuta labari sun kai kamar guda nawa?
Labarai biyar gare ni daga lokacin da na fara zuwa yanzu daan lokacin dana fara ina rubutawa a takarda kafin na mallaki waya na rasa da yawa daga cikinsu.
Ya farkon farawarki ya kasance?
Gaskiya farkon fara rubutuna bai zo mini da wata matsala ba, kasancewar kafin na fara na zurfafa bincike sosai a harkar, har na tsinci wasu ilmin tun kafin na ma fara.
Wane labari ne ya fi baki wahala wajen rubutawa?
‘Matan Arewa’ Gaskiya shi ya fi bani wahala, domin rubutu ne mai fadi sosai da ya kunshi abubuwa da yawa musamman akan mata da irin rayuwar da suke fuskanta a arewa.
Kin taba buga labarinki?
A’a babu sai dai niyya.
Wanne irin nasarori ki ka samu game da rubutu?
Alhamdulillah na samu nasarori sosai musamman addu’o’in jama’a, na dauki hakan babban nasarar da kudi ba za su saya min su ba.
Ya ki ka dauki rubutu a wajenki?
Na dauki rubutu wata hanyar isar da sako ga jama’a mai cike da hikima.
Mene ne burinki na gaba game da rubutu?
Burina a rubutu shi ne sakon da nake son isarwa su kai inda kafafuna ko muryata basu da damar zuwa, domin ban fada harkar rubutu don zama sananniya ko kuma domin bidar shahara ba, illa iyaka son bada tawa gudumawar ga al’umma ta hanyar ruwan alkalamina.
Bayan rubutu kina wata sana’ar?
Eh! ina harkan ‘Graphics’.
Ya ki ke iya hada rubutunki da kuma sana’arki?
Kowanne da lokacinsa kuma babu wanda yake shiga lokacin wani.
Kamar da wanne lokaci ki ka fi jin dadin yin rubutu?
Safe da kuma yammaci don sam bana yin rubutu da rana.
Me za ki ce da masoyanki?
Babu abin da zance dasu face godiya na gode da soyayyarsu gare ni Allah ya bar zumunci da kauna tsakaninmu.
Ko kinada wadanda za ki gaisar?
Da farko iyayena Alh.Tijjani Iyam da kuma malama Aisha Ishak Fada, sai kuma Ahmad Toshiba wanda ya zamto tamkar dan uwan da muka fito ciki daya dashi wanda harkar rubutu ce ta hada mu, sai kuma ‘yan uwa da abokan arziki da makaranta littattafaina