Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana matukar takaicinsa da cin fuska da hukumomin Libya suka yi wa tawagar wasan kwallon kafar Super Eagles da suka ziyarci kasar.
Shugaban wanda ya yaba da dawowar tawagar gida lafiya, ya bukaci hukumar da a da ladabtarwa ta Hukumar Kwallon Ƙafar Afirka (CAF) da ta gudanar da sahihin bincike domin bayar da shawara a kan matakin da ya dace a dauka a kan wadanda suka saba wa dokokinta.
- Gwamnan Zamfara Ya Rantsar Da Shugaban Hukumar Zaɓen Jihar
- Gwamnatin Tarayya Ta ÆŠaga Likkafar Filin Jirgin Saman Maiduguri
Tinubu ya yaba da hadin kan da aka samu wajen aiki tare tsakanin ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya da takwararta ta wasanni domin magance matsalar da aka samu, da kuma dawowa da ‘yan wasan gida cikin koshin lafiya.
Tinubu ya jinjina wa ‘yan wasan saboda jajircewarsu duk da irin halin da suka samu kansu a Libya.
Yayin da yake bayyana kwallo a matsayin wasan da ke hada kan jama’a da kasashe.
Tinubu, ya ce irin wulakancin da aka nunawa ‘yan wasan Super Eagles da kuma jama’arta ya saba wa dokokin da aka gindaya.
Shugaban ya bukaci duk masu sha’awar kwallon kafa da masu tafiyar da ita da su hada kai domin aiki tare don kaucewa irin wannan yanayi nan gaba.