Kabiru Abubakar Aliyu, wanda aka fi sani da Nakwango, ɗaya daga cikin manyan dattawan Kannywood, ya bayyana yadda ya fara harkar fim tun shekarun 1970 a wasan kwaikwayo, sannan daga baya ya shiga fim a shekarar 1994/1995. Ya ce a farkon lokaci yana fitowa a matsayin mace saboda murya tana da laushi.
Fim ɗinsa na farko shi ne Kilu ta Ja Bau na Hamisu Iyantama, sannan a 1995 ya fito a fim ɗin So ne ko Kauna ƙarƙashin kamfanin Dabo Films, wanda ya zama fim na farko a Hausa da aka nuna a sinima a Kano.
- Masana’antar Kannywood Na Tsananin Buqatar Addu’a – Hauwa Garba
- Na Yi Lokacin Da Idan Aka Gan Ni Ake Gudu A Masana’antar Kannywood – Mai Dawayya
Nakwango ya yi watsi da zargin cewa duk ƴan fim marasa tarbiyya ne, yana mai cewa “a kowace sana’a akwai nagari da marasa nagarta.” Ya bayyana cewa dalilin da yasa ya rage fitowa a fina-finai shi ne saboda yanzu yawancin fina-finai ba sa ɗauke da darasi na addini ko na al’ada. Ya ce sai dai idan fim ya shafi kira ga Allah da nuna al’adun Hausawa zai shiga.
Ya kuma soki fina-finai na zamani da ya kira “fina-finan harshen Hausa” ba “fina-finan Hausa na gaske” ba, saboda rashin nuna al’adu da tsaftar harshe. Ya ce ana yawan gauraya Hausa da Turanci tare da kawo tashin hankali da kwaikwayon Turawa, abin da ke rushe ƙimar masana’antar.
Duk da haka, ya tabbatar da cewa bai taɓa nadamar shiga harkar fim ba, domin ta ba shi girmamawa da albarka da ba zai manta ba, har da lokutan da mutane suka taimaka masa saboda sun san shi a fim.
Fitaccen ɗan wasan ya tuna wani lokaci da aka kama shi bayan ya tsaya wa wani a kotu wanda ya gudu, amma aka sake shi saboda shahararsa. Duk da ɗansa na daga cikin manyan masu gyaran hotunan Fim (editing ), ya ce matsayin da Allah ya ba shi a harkar fim alheri ne na ƙaddara.
Ya shawarci abokan aikinsa da su ji tsoron Allah, su riƙa kare addini da al’adu, sannan su yafe wa juna. Ya kuma roki al’umma da kada su gaggauta yanke hukunci kan masu fim.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp