A wanan makon wakiliyarmu Bushira Nakura ta tattauna ne da Sahura Haruna Isma’il Meguza wata mai sana’ar sayar da maganin mata, ta yi bayanin yadda ta samu kanta a cikn sana’ar da kuma irin kalubalen da ta fuskanta a yayin da ta fara sana’ar da kuma burin da take da shi a nan gaba.
Ga dai yadda hirar ta kasance:
Da farko masu karatu za su so su ji cikakken sunanki da kuma sunan da aka fi saninki da shi, tare da dan takaitaccen tarihinki.
Sunana Sahura Haruna Isma’il Meguza, an haifeni a Fage ashekarar 1987, na yi karatun addini dana Boko daidai gwarwadon iko.
Me ya ja hankalin ki har kika fara sana’ar sayar da magungunan mata?
Ai ita wannan sana’a ce me cike da lada da kuma daidaito ga ma aurata gefe guda kuma sana’a ce da zaka sami rufim asiri.
Ya farkon fara sana’arki ta kasance,ta wacce hanya kika bi har kika fara, kuma ya kika ji a lokacin da zaki fara, kasancewar wasu na son yin irin sana’ar amma kuma suna tsoro ko kunya, shin kema kin tsinci kanki a irin wannan matsalar ko kuwa?
Tabdijan a lokacin da zan fara don ba komai ma na iya ba saidai na je gun yayata na karbi magungunan da yawa na yi wasu da kaina na hada nazo na jerasu a kan tebur sai mata masu sari da masu siyan daidai su fara dauka wasu su kawo kudi daidai wasuma bazan sake ganinsu ba.
Gaskiya ban ji kunya ba tunda mu munga wasu daga iyaye mu da yayye suna yin wannan sana’ar mun taso a cikinta gaskiya, in ana maganar kunya sai wanda ya shigo harkar kai tsaye shi ne zai rinka jin kunya kafin ya waye a ciki.
Daga lokacin da kika fara sana’ar kawo yanzu za ki kai kamar shekara nawa kina yi?
To a yanzu dai gaskiya daga lokacin dana fara sana’ar magani zan kai shekara 16 in ma ban fi ba.
Ke kike hada magungunan da kanki ko kuwa sarowa kike yi, sannan ke ma ki dora naki ribar ki sayar, ya abin yake?
Alhamdulillahi yanzu kam ni nake yi, sai dai wani abin bani dashi na kan sara daga wasu.
Ya kike ganin yadda karbuwar sana’ar take kasancewa ga su masu sayan, shin kwalliya na biyan kudin sabulu kuwa?
Alhamdulillahi, a gaskiya sana’ar indai za a yi aiki me kyau to ba damuwa za ta karbu , gaskiya kwalliya na biyan kudin sabulu.
Ta wacce hanya kike bi wajen ganin kin bunkasa kasuwancinki?
Ta hanyoyin sadarwa (social media) Facebook, WhatsApp, TikTok, dadai sauransu.
Za ki ji likitoci da wasu masana na magana game da ire-iren wadannan magunguna wanda mata ke amfani da su, na cewar suna iya kawo wa mace matsala, me za ki ce a kan hakan?
Haka ne ai akwai wanda basu san me suke ba su dai kawai su sami kudi, yana da kyau kowace mace tasan me za ta saya tai amfani da shi ta san kuma daga wa ta saya gudun samun matsala.
Wanne irin kalubale kika taba fuskanta ga su masu siyen, musamman wajen karbar bashi kuma aki biya, ko kuma a saya a samu matsala, ko makamancin haka, me za ki ce a kan hakan?
To gaskiya na fuskanci kalubale da dama a yanzu haka akwai wayanda suka sa na tura musu kaya da zummar in sun karbi kaya za su sami kudin amma har yau ba amo ba labari wata ma ta yi ‘Blocking’ dina haka na hakura kuma ba kudi kadan ba, masu kanana ma kuwa ba’a magana.
Wadanne irin nasarorin kika samu game da wannan sana’a taki?
Alhamdulillahi na samu nasarori da dama da ba za su kirgu ba sai dai muce Alhamdulillahi.
A ina kike gudanar da kasuwancinki, akwai wani waje ne da kika ware na musamman ko kuwa a cikin gida kike yi?
Ina yi a gida da kuma ‘Social media’ kamar yadda na fada miki tun da farko
Mene ne burinki na gaba game da wannan sana’a taki?
Allah ya kara sa mana albarka a sami babban shago asa kayyakimmu a samin masu kula da gurin
Kamar wanne abu ne ya taba faruwa da ke na farin ciki ko akasin haka wanda ba za ki taba mantawa da shi ba?
Mace ta farko dana taba turawa maganin kashe meku ya wato (kaikayi da kurajen gaba) kamaru ta yi min kyautar danayi mamaki, dama dana gaya mata kudin magani ta ce ita ba kudin take son jiba indai na tabbatar magani mai kyau ne in biya kudin mota in aika mata haka na biya na aika Aiko naji dadin godiyar da tayi da jin dadin data yi sannan ta yi min ninkin bani kin kudin abin dana aika mata na ji dadi kuma na yi farin ciki.
Bayan sayar da magunguna da kike yi, shin kina wata sana’ar ne ko iya ita kawai kike yi?
Na dan taba rubutun littafi kuma yanzu haka ina hadawa dasu turaran wuta dana humra.
Idan kina wata sana’ar ya tsarin kasuwancin yake kasancewa, kuma ya bambancin yake kamar wajen yadda sana’ar take kawo kudi da sauransu?
Akwai bambanci mabayyani gaskiya domin shi magani dabanne wata daga uwa duniya zatace naki takeso gaskiya magani yafi tafiya yadda akeso
Wanne kira za ki yi ga matasa musamman mata wadanda ba sa sana’a ba su da abin yi, har ma da manya na gida, me za ki ce a kan su?
To sana’a dai rufin asiri ce musamman ma ga mata domin tallafawa iyayenki, ‘Yan uwa, mazajen da yara Dake kanki domin in kina sana’a ba sai kinyi yar mirya abakiba hasalima ke Zaki tallafi wasu, suttura da kayan kwalliya da Kawa sai Wanda kika so.
Ko akwai wani kira da za ki ga gwamnati game da masu kokarin yin sana’a?
A tallafa musu don su samu su tsaya da kafafunsu.
Me za ki ce da wannan shafi na Adon Gari?
Godiya ta musamman ga wannan shafi na adon gari
Me za ki ce da Jaridar Leadership Hausa?
Allah ya kara daukaka wannan jarida ta LEADERSHIP HAUSA kuma Allah ya karo dumbin masoya ya biya musu bukatnsu na alheri na gode.
Ko kina da wadanda za ki gaisar?
Gaisuwa ta musamman ga iyayena, yayata Maman Nura me kayan mata, kanwata Maman Al-ansar jigon mata,da sauran ‘yan uwa da abokan arziki da kuma Malama Bushira Nakura. Na gode
Muma mun gode